Amfanin Ganyen Shuwaka Ga Lafiyar Jiki.

1 1,700

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Amfanin Ganyen Shuwaka, ganye ne mai daci mai kuma matuƙar magani ga lafiyar jikin ɗan adam wadda akan iya kiranta da turanci Bitter Leaf sai kuma sunanta na kimiya wato vernonia amygdalina, shuwaka tana tsirowa a mafi yawan ɓangarorin Afirka, ana amfani sosai da ita a gargajiyan ce.

A tarihance, ana amfani da ganyen a matsayin magani don cutuka da yawa daga zazzaɓin cizon sauro, taifod, ciwon sukari, gudawa, tarin fuka, gallstone da cutar koda, zuwa rigakafin cutar kansa da rage hauhawar jini.

Hakanan an tabbatar da ganyen yana ɗauke da abubuwa kamar su antibacterial da antifungal. Wannan dalili na muhimmancin shuwaka yasa shafin Alummarhausa bincike don kawo muku amfanin ta ga lafiyar jiki.

  • Ganyen Shuwaka Yana Taimakawa Magance Ciwon Ciki.

Shuwaka magani ne na gargajiya don ciwon ciki. Wani bincike a cikin mujallar Toxicology Reports ya nuna cewa tsiron na iya bada kariya daga cutar Olsa. Binciken ya nuna cewa antioxidants dake cikin shuwaka suna ba da gudummawa ga tasirin waɗannan cutuka.

  • Tana Bada Kariya Daga Cutar Kansar mafitsara

Ciwon Kansar mafitsara cuta ce wacce yawanci tafi kama maza musamman mazan da suka manyanta. Duk da yake bin magungunan da wani ƙwararren likita ya tsara suna da mahimmanci don cin nasara don magance ƙwayar cutar, Shuwaka na bada gudunmawa matuƙa wajen kare kai daga kamuwa da wannan cuta.

  • Ganyen Shuwaka Na Taimakawa Wajen Magance Rashin Bacci.

Sauda dama wasu kan kasa yin bacci da dare sakamakon wani damuwa ko tunanin wani abu daban.

Shan ruwan shuwaka da daddare, kafin kwanciyar bacci zai kawo nutsuwa da annashuwa wanda yake taimakawa wajen samuwar Isasshen bacci.

  • Ganyen Shuwaka Na Samar Da Ƙwayoyin Haihuwa

Wani bincike a cikin International Journal of Reproductive Biomedicine ya nuna cewa shuwaka na iya samar da sakamako mai kyau kan ingancin maniyyi. Gabaɗaya, yawan sindaran dake cikin Shuwaka suna da amfani ga lafiyar gaban namiji, don haka zai zama da amfani ga ma’aurata masu ƙoƙarin ɗaukar juna biyu yin amfani da ita a ko yaushe.

Shuwaka tana ɗauke da flavonoids, wanda ke da tasirin antioxidant, kuma suna taimakawa tare da magance matsaloli daban-daban na lafiya kamar zazzabi mai zafi. Musamman, ana amfani da ganyen shuwaka a tarihin gargajiya don maganin ƙwayoyin cuta na zazzaɓin taifot da zazzaɓin cizon sauro.

  • Tana ɗauke Da Sinadarin Da Zasu Iya Taimakawa Mai Cutar Sikari

Shuwaka na iya taimakawa mai ciwon sukari. Binciken da aka buga a cikin Jaridar Kimiyyar Halittu ya nuna cewa kasancewar kwayoyin halitta, bitamin da sauran abubuwan gina jiki kamar sunadarai, lipids, carbohydrates, ash da sauran abubuwan da ake hadawa ana tunanin za su yi aiki tare don rage ƙarfin sukarin dake jiki mutum.

  • Shuwaka tana Da Sunadarai Da Zasu Iya Taimakawa Masu Hawan Jini
  • Shuwaka na da kyau ga ƙashi da haƙora

Vitamin C babban ma’adanai ne na antioxidant da ake samu a cikin shuwaka wanda ke taka muhimmiyar rawa a cikin jiki, gami da kula da ƙasusuwa da haƙori.

Hakanan yana dauke da sinadarin bitamin K wanda yake taimakawa jiki kula da lafiyar kasusuwa kuma tana hana raunin kashin nama, wanda aka fi sani da osteoporosis.

  • Yana taimakawa wajen yakar cutuka marasa tsari

Wani sinadarai a cikin shuwaka shine bitamin E, wanda ke aiki a zaman antioxidant tana yaƙi da ƙwayoyin cuta waɗanda ke da lahani jikin dan adam.

Abin Lura:

Yadda ya kamata kayi amfani da ganyen Shuwaka a gargajiyan ce shune, zaka iya amfani da Shuwaka ta hanyar tauna ɗanyun ganyen ka haɗiye ruwan. Ko kuma, zaku iya daka danyen ganyen a cikin turmi kuma a fitar da ruwan. Zaku iya sa ɗan gishiri a ciki.

Kada a manta koyaushe ka tuntuɓi likitanka game da duk wata damuwa ta likita, yanayi da kari da zaka iya sha. Koyaushe ɗauki shawarar ƙwararren likita game da yadda zaka ci gaba da jinyarka

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Zahra Muhammad says

    Allah yasaka DA alkairi

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »