AMFANIN KARAS A JIKIN DAN’ADAM DA MAGUNGUNAN DA YAKEYI

0 2,670

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

karas na daya daga cikin kayan lambu wadanda muke amfani dasu wani zubun muci har musanya a abincin, saidai wasu basu san mainene mahimmancin sa ba,ALUMMAR HAUSA munyi maku bincike akan amfanin da karsa keyi a jikin dan adam da kuma magungunan da yakeyi na cututtuka

1. YANA GYARAN JIKI

Karas na dauke da sinadarai masu yawa da ake kira ‘carotenoids’. Binciken kimiyya ya nuna cewa ‘ya’yan itatuwa da ganye suna dauke da sinadarai na ke inganta lafiyar mutum ya kuma haskaka fatarsa ya. Sai dai cin karas din fiye da kima yana iya haifar da matsala mai suna ‘carotenosis’ da ke saka fatar mutum tayi haske da yawa.

2. YANA RAGE KITSE A JIKIN DAN’ADAM

Cin karas yana rage kitse a jikin dan adam da kuma kara sinadarai masu yaki da cututtuka. Hakan na inganta lafiyar zuciya. Danyen karas na kunshe da lectin da ke taimakawa wurin rage cholesteral.

3. CIN KARAR NA TAIMAKAWA JIKI WAJEN KIYAYEWA DA KAMUWA DA CIWON DAJI (cancer)

Karas na dauke da wasu suna darai masu yawa da masana ke kira ‘Phytochemicals’ da ke yaki da cutan daji. Wasu daga cikin sinadaren sun hada da beta-carotene da sauransu. Wadannan sinadaren na karfafa garkuwar jiki. Masana sun kuma gano karas na iya maganin Leukemia da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji na baki.

4. INGANTA LAFIYAR HANTA

Karas na dauke da glutathione, wani muhimmin sinadari da ke kawar da ababen da ke cutar da hanta. Karas har ila yau na dayke da beta carotene da Vitamin A da ke inganta aikin hantar dan adam da kare ta daga cututtuka.

5. KARAS NA TAIAMAKAWA MASU CIWON SUGA

Bincike ya nuna cewa Vitamin A na kare afkuwa da kamuwa da ciwon suga kuma tunda karas na kunshe da sinadarin sosai yana iya taimakawa. Cin abinci mai inganta lafiya yana taimakawa wurin rage kiba da kuma hana kamuwa da ciwon suga nau’i na biyu.

6. KARA KARFIN KASHI

Beta-carotene da karas ke dauke da shi yana kare kwayoyin hallita daga cututuka kuma yana taimakawa inganta lafiyar kashi. Vitamin A yana taka muhimmiyar rawa wurin gyara kashin dan adam.

7. CUTUTTUKAN BAKI DA HAKORI

Danyen karas yana taimakawa wurin kawar da kwayoyin cuta daga hakora kuma ya washe numfashin mutum. Fibre da karas ke dauke da shi yana kara adadin yawu a bakin mutum da ka iya taimakawa ya rage adadin citric acid a malic acid da ke bakin dan adam.

8. BUGUN ZUCIYA

Wani sabon bincike da masana kimiyya suka gudanar ya nuna cewa ruwan da aka tatsa daga karas na rage hawan jini da kashe 5 cikin 100. Sinadaren da ke cikin karas da suka hada da potassium,fibre, nitrates da Vitamin C ne ke taimkawa wurin wannan.

9. YANA KARA KARFIN GARKUWAN JIKI

Vitamin A yana taimakawa wurin aiwatar da wasu ayyuka a jiki tare da kare cututtuka. Hakan na yiwuwa ne saboda yana inganta garkuwar jikin mutum. Karas kuma na dauke da Vitamin C da shima ke karfafa garkuwar jiki.

10. INGANTA LAFIYAR IDO

karas na dauke da Sinadarin Vitamin “A” wanda yake taimakawa idanu su rika gani tangaran kuma karas na dauke da wannan sinadari na Vitamin A masu yawa.

wadannan sune kadan daga cikin amfanan da karas keyi a jikin dan’adam fatan kucigaba da kasancewa damu don samin Ingattatun shirye shiryenmu na fannin magunguna, tarihi, da fadakarwa da sauransu mungode fatan za’ai share domin mutane su amfana

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »