Taƙaitaccen Tarihin Mawaƙi Nura M Inuwa.

1 3,095

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nura Musa Inuwa wanda aka fi sani da Nura M Inuwa. An haifeshi a ranar 18 ga watan Satumbar shekarar alif 1989, a Gwammaja dake ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano dake Najeriya.

Nura M Inuwa yayi karatun sa na Firamare a Masaƙa wato Masaƙa Sapecial Primary School. Yayi karatun sa na Sakandare a Gwammaja 2.

Mawaƙin bai cigaba da karatun gaba da Sakandare ba ya kama harkar waƙa.

Mawaƙi Nura ya fara waƙa ne tun yana ƙarami wanda hakan har Allah yasa itace harkar cin abincinsa.

Nura ya shaidawa manema labarai cewa yana da waƙoƙi dayawa wanda suka haɗa dana fina finan Hausa, na Siyasa, na Soyayya dadai sauransu, wanda ya rere kuma mawaƙin yace shi ba’a rubuta masa waƙa duk komai shi yake kayansa.

mawaƙina nada manyan abokai ciki harda Adam A Zango jarumi a masana’antr shirya fina finan Hausa dake kano

M Inuwa yasamu kyaututtuka da dama kamar su.

Karamawar ƙungiyar Dalibai
  • City People Entertainment Award: Gwarzon Mawaƙi a shekarar 2014, da ake gudanarwa a shekara shekara,
  • City People Movie Award: Gwarzon mawaƙin kannywood a shekarar 2017,
  • Muryar Hausawa Award a shekarar 2020. Dadai sauransu.

M Inuwa yayi aure a shekarar 2017, inda ya auri matarsa mai suna Amina, da ƴarsu daya mai suna A’isha amma anai mata laƙabi da (Farrah)

Farrah m inuwa
Farrah m Inuwa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. ayuba mamuda says

    Your Commentfans

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »