Tarihin Marigayi Mai Martaba Sultan Saddiq Abubakar III

2 838

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai martaba Sultan Saddiq Abubakar III a shekara ta alif 1903 zuwa alif 1988 ya kasance shugaban musulmin Nijeriya wanda ya yi sarautar Sarkin Musulmi daga shekarar alif 1938 zuwa 1988.

An haifeshi a garin Dange, a ranar 15 ga watan Maris, 1903, a ranar da turawan mulkin mallaka suka fatattaki Mulkin Halifancin Sokoto. Shi ɗa ne ga Usman Shehu, jikan Mu’azu, kai tsaye daga zuriyar Uthman Dan Fodio yake.

Abubakar yana da Ilimin Addinin Musulunci. Ya rike mukamai da dama kafin ya gaji kawunsa, Hassan Ibn Mu’azu, yana da shekara 35.

A shekarar alif 1938, an naɗa shi kansila na karamar hukuma na Gwamnatin Yankin Sakkwato a Talata Mafara wanda yanzu take a Jihar Zamfara.

Ya ƙaware wajen iya mulki da kuma yadda ya dace da ruƙo daga kotunan gargajiya da kuma kula da hakimai da shugabannin ƙauyuka.

Ya kasance Sardaunan Sokoto har zuwa ranar 17 ga watan Yuni, shekarar alif 1938, lokacin da ya zama Sarkin Musulmi Abubakar III.

A matsayinsa na Sarkin Musulmi na 17 kuma, ya zama mafi mahimmancin halayen Musulunci a kudancin Sahara, kuma ana girmama shi sosai.

Ya kasance shugaban mabiya miliyan 50 masu bin addinin Musulunci a Afirka ta Yamma.

Turawan Ingila sun karamashi a matsayin jarumi a shekarar alif 1944, kuma bayan da Najeriya ta samu ‘yanci,. Gwamnatin Tarayya ta sanya shi Babban Kwamandan Kungiyar Order of Niger (GCON).

Ya yi mulkin masarautar ne a daya daga cikin mafi dadewa a tarihi, daga ranar 17 ga watan Yuni, shekarar alif 1938, zuwa 1 ga Nuwamba, shekarar alif 1988,. Lokacin da ya mutu, yana saura watanni huɗu da yin murnar bikin cika shekara ta 50 a kan karagar mulki.

Abubakar ya mutu ya bar ƴaƴa 52 da jikoki 320.

Allah yajiƙan da.
Alummarhausa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Abdullahi Sani Total says

    Your Comment Allah Ya jikan shi da rahama.

    1. alummarhausa says

      Amin Thuma Amin

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »