Nuhu Abdullahi Balarabe da akafi kira da Nuhu Abdullahi na daya daga cikin Jaruman Kamfanin Shirya Fina-finan Hausa dake Kano, dakum kamfanin shirya fina-finan turanci dake kudu.
An haifi Nuhu Abdullahi ranar 3 ga watan Janairun shekarar alib 1991, a jihar Kano dake Najeriaya.
Jarumin ya shiga Kamfanin Shirya Finafinan Hausa dake Kano a shekarar 2009, a matsayin mai shirya Fim inda ya samar da finafinai kamar su Baya da Kura,
Fulanin Asali, Kuskure, Mujarrabi da kuma wasu finafinai dadama.
Jarumin ya fara fitowa a wasan kwaikwayo a wani fim mai suna Ashabul Khafi, Nuhu yayi suna sosai saboda fitar wani fim mai suna Kanin Miji.

Jarumin ya fito a finafinan turanci dadama ciki akwai irinsu There’s Way, Light and Darkness, Thorny, Heart Beat dadai wasu dama.
Nahu Abdullahi yasamu kyaututuka ciki harda City Entertainment Award a shekarar 2015, saikuma Africa Magic Viewers choices Award a 2016 dadai sauransu.
A ranar 4 ga watan Disamba na shekarar 2020 ne jarumin yay aure ga zan kaɗeɗiyar matarsa mai suna Jamila Abdulnasiri (Siyama). Daga ƙasa ga kaɗan daga cikin hotunan bukin.
[…] to the internet it was reported that Nuhu Abdullahi make anywhere from N500,000 to N1 Million depending on the […]