Yadda Zaa Magance Cututtuka Dake Jikin Dan Adam Ta Hanyar Amfani Da Suratul Fatiha.

1 3,015

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Fatiha Surace Mai Girman Matsayi da’a keyi Mata Kinaya ko kirari da Uwar Alƙ ur’ani, Ana yi Mata Laƙabi da Surar Budi,

Wannan budin nata yasa wani malami ya jero mana wasu muhimman bayanai nadaga cikin Surar wanda cikin yadar Allah da hukuncinsa idan akayi amfani da surar za’a samu waraka na cututtuka dake damun mu a wannan zamani.

Ina fata ka/ki tsaya ki nutsu wajen sauraron wannan bayani.

Ciwon Kai
Komai Tsananin Shi Kasa Hannun ka Na Dama Ka Kama Goshin Ka, Ka Karanta Fatiha 7, Zai Sauka,

Ciwon Haƙarƙari
Akaranta Fatiha 7 A Tofa A Hannun Dama A Shafi Haƙarƙari Ciwon Zai Dauke da yardar Allah

Ciwon Idanu
A Gyara ƙayar Aduwa ta Zama abin Shafa Kwalli, A Karanta Fatiha 1 Atofa a Jikin ta A Shafa Kamar Kwalli a Idon da yake Ciwon, Kayi Haka Sau 3 A Rana Har Kwana 3, Za’a Sami Lafiya,

Ciwon Ciki
A debi Ruwa da Ludayin Miya A Karanta Fatiha 7 Atofa Asha, Za’a warke da yardar Allah,

Ciwon da yake Yawo Ajiki
Arubuta Fatiha 71 A wanke da Ruwan Sama Asha ashafe Jiki Zaa Sami Lafiya da yardar Allah,

Sihiri
Wanda Maƙiya Suka jefa, a Rubuta Fatiha ƙafa 33 a wanke da Ruwan Sama, A Karanta Fatiha ƙafa 33 a Tofa Cikin Rubutun Asha A shafe Jiki, Za’a ku6uta Daga Jifan

Mace Mai Naƙuda
A Karanta Fatiha 11 A Tofa a Ruwan Dumi Abata Tasha, Zata Sauka Nan Take da Yardar Allah

Mai Ciwon Ƙashi
Fatiha ƙafa 3 Ana Tofawa a WajenZa’a Nemi Ciwon Arasa,

Masu Aljanu.
Idan Iska ta Taso Ajikin Mutum A Karanta Fatiha 7 A Tofa a Ruwa A Fesa a Fuskar Shi, Nan Take Za Su Sake Shi

Rubutawa:

IMAM ADAMU

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Abubakar mustapha says

    Masha allah

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »