Tarihin Shieck Shehu Abdulkadir Zariya

0 2,200

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


Malami ne ga Sheik Dahiru Bauchi da Sheik Abubakar Chiota

Tarihi ya nuna babu mutumin da ya yada ilimin addinin musulunci a kabilar Nufawa kamar Shehu Abdulkadir Zaria

An haifi Shehu Abdulkadir Zaria a garin Agaie dake jihar Neja a shekarar 1909, shekaru dari da sha daya (111), ya taso a gidan karatu domin mahaifinsa malami ne mai karantarwa a allo da ilimi.

Bayan ya girma Allah ya sa mishi son yin karatun ilimi mai zurfi, hakan ya tursasa mishi barin mahaifarsa, garin Agaie zuwa kasashen hausa dan neman ilimi mai zurfi.

Bayan ya zama teku a fannonin ilimin addinin musulunci kama daga Fiqhu, Nahwu, Balaga, Sarfu, Lugga, Mandik, Qur’an da Hadisi(ruwaya da diraya), Tajwidi, Arud, da Tauhidi sai ya zo Zariya inda ya kara karatu kuma Allah ya nufe shi da zama a Zariya, inda ya kafa babbar jami’rsa ta ilimin addini a Anguwan Limancin Iya, dalibai daga fadin Najeriya da kasashen ketare sukai ta tururuwar zuwa neman ilimi a wannan jami’ar ta sa.

Daga nan sai Shehu Abdulkadir Zariya ya koma garin Agaie inda yake zuwa lokaci lokaci, yayi jihadi ya rabasu da wasu munanan al’adu na jahilci da suke aikatawa kamar rashin kullen mata da rashin riko da addini da tsafi, ya kuma yada ilimin addini a cikin al’umar Nufawa, saboda Shehu ya shiga kauyuka da birane kwararo kwararo na Nufawa tsakanin Neja da Kwara da Kogi yana shiryar da su bin tafarkin shari’a madaidaiciya. A sanadiyyarsa dubannin nufawa sun zamo malamai, a yanzu dai zai yi wuya ka samu wani Malami banufe a yankin Neja da Kwara da Kogi wanda a karatunsa bai da alaqa da Shehu Abdulkadir Zaria. Ba iya nan ba Kusan a fadin Najeriya babu jihar da bai da almajirin da ya koyar ilimi.

Yana daya daga cikin malaman da suka sallamawa maula Shehu Ibrahim Inyass RTA. Shi ya kawo Shehu Ibrahim Inyass garin Zariya.

Bayan karfafa darikar tijjaniyya a yankin nufawa, shi ya kai faidar Shehu Ibrahim Inyass yankin wanda yanzu za’a iya samun nufawa sama da miliyan wadanda suke danganta kansu da faidar Shehu RTA. .

Ya wallafa littafai da dama a fannonin ilimi kamar Fiqhu da Yabon manzon Allah saw da fannin Ilimin Alqur’ani da Sufanci.

Ya bar duniya a shekarar 1980. Wadanda suka gaje shi bayan wafatinsa daga cikin almajiransa akwai ‘ya’yansa kamar haka :

  1. Khalifa Sheikh Tijjani Abdulkadir Zaria
  2. Sheikh Sani Khalifa Abdulkadir Zaria
  3. Sheikh Yusuf Sheikh Abdulkadir Zaria

Daga cikin almajirai akwai :

  • Sheikh Idris Fogun Bida
  • Sheikh M. Nasiru Sheikh Abdulkadir Zaria
  • Sheikh Fadalu Gwargwaje
  • Sheikh M.Magaji Banufe
  • Sheikh M. Idi Kaura
  • Sheikh M.Sani Dandume

Daga cikin almajiransa wadanda suka yi fice a duniya akwai :

Maula Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya yi karatun ma’arifa da azkarul tarbiyya a wajensa.

Maula Sheikh Abubakar Chiota RTA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »