Tarihin Alhasan Dantata

0 2,627

Tarihi Alhassan Dantata A Takaice

An haifi Alhassan Dantata a shekarar alib 1877. Yana daya daga cikin zuriyar Agalawa kuma dukkan zuriyarsu ‘yan kasuwa ne kuma mashahuran masu arziki . Zuriyar Ali Madugu dan Abdullahi mahaifinsa Madugu Baba Talatin.

Ya fara karatun allo a garin Bebeji a makaranta wadda take karkashin darikar Tijjaniyya.

Madugu Baba Talatin ya taso ne daga jahar Katsina a cikin karni na sha tara ya dawo Kano inda ya sayi gidansa a Bebeji kuma a nan aka haifi Alhassan Dantata. Ya koma garin Madobi daga nan ya bar Dantata da Mahaifiyarsa ya wuce Gonja. Bayan ya komo ne kuma ya zabi ya koma garin Bebeji da zama, A can ya zauna har karshen rayuwarsa.

Mahaifinsa ya rasu yana dan shekara bakwai a duniya. A wancan lokacin saboda karancin shekaru ba za su iya daukar ragamar kasuwancin mahaifinsu ba bayan an raba musu gado.

Mahaifiyar Alhassan ta koma Accra ta kasar Ghana inda ta bar Alhassan a karkashin kulawar hadimarta mai suna Tata. Tata ita ta zama uwa a wajen Alhasan. Kuma Alhassan ya samo lakabin sunansa ne daga sunan wannan hadimar mahaifiyar tasa Tata. Don ita ake ce masa Dan Tata.

Mahaifiyar Alhassan Dantata kamar mijinta ‘yar kasuwa ce mai arziki mashahuriya wajen saye da sayarwa.

Duk da Alhassan ya koma Accra wajen mahaifiyarsa daga baya ya koma Bebeji. Lokacin da yakin Basasar Kano ya barke Alhassan da ‘yan’uwansa Bala da Sidi sun shiga hannun Ningawa sai daga baya aka gansu.

Bayan mutuwar mahaifiyarsa a shekarar 1903 Dantata ya mayar da hankalinsa kan kasuwanci daga Kano zuwa Lagas a wannan lokacin ne ya gina gidansa na unguwar Sarari a cikin Koki.

A cikin alib 1918 ne Turawan kamfani suka neme shi ya zama daya daga cikin dilolinsu a lokacin suna kasuwancin gyada da goro. A shekarar alib1922 an yi ittifakin kaf Kano babu mai arzikinsa . Ya ba da zunzurutun kudi har fam 10,200 dan gina masaka a arewacin Najeriya.

A shekarar alib 1955 Alhaji Alhasan Dantata ya kwanta rashin lafiya, kasancewar tsananin rashin lafiyar da yake ciki sai ya kirawo babban mai kula da harkar kudinsa Garba Maisikeli da kuma yayansa. Ya sanar musu cewa shi yana ganin lokacin komawa ga mahaliccinsa yayi don haka su rayu da yan uwansu cikin lumana da kwanciyar hankali. Sannan yace musu suyi aiki tukuru wajen ganin kamfanin sa na (Alhassan Dantata & Sons) bai karyeba.

Sannan ya shawarce su kansuyi kokarin yin Auratyya a tsakaninsu, sannan yace musu suyi kokarin taimakawa yan uwansu musanman wadanda basu dashi. kwana uku da yin wannan nasihar ya rasu yayin da yake bacci a ranar Laraba 17 ga watan Agustar shekarar Alib 1955. An kuma binneshi a gidansa dake Unguwar Sarari Allah ya kyauta makwanci Amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »