Yadda Zaa Kawar Da Kurajen Fuska Ko Tabon Da Yayi Baki.

1 17,628

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Domin Kawar da kuraje fusaka

Kurajen fuska kurajen da kan fito a fuska, yawancin sukan fito suyi ruwa bayan ruwan kuma sai suyi tabo maana sai fuskar mutum tayi baki baki wanda hakan kasanya kaga mutum fuskarsa tayi kala biyu wani wurin baki wani wurin fari. Kuma wannan matsala galibi tafi faruwa ga mata.

Bakin tabo kuma yana samuwa ne yayin rauni ko kurji ya fitoma a wani wuri daban ba lallai sai a fuskarka ka ba.

To insha Allah Allah wannan magani da zamu bayar indai anyi amfani dashi yadda ya kamata to zaa samu waraka bi’izinillah.

Abinda Za’a Nema.

  • Ganyen Na’a Na’a
  • Lemon Tsami ,

Yadda za’a hada

Da farko zaki kirba ganyen Na’a Na’a dinki a turmin karfe , sai azubashi a Kofi ko kwano, sai a matse ruwan Lemon tsamin a ciki ganyen da kika kiraba na Na’a Na’a din saiki Juya sosai.

Zaki dinga shafa shi a inda matsalar take har na tsawon Mintuna 40, saiki wanke Insha Allah za’a dace . Kuma yana gyara fatar jiki sosai.

Hanya Ta Biyu Da Zakibi.

Hanya ta biyu da zakibi don magance kurajen fuska ko tabon fuska shine.

Dafarko zaku samu Alobera dinku mai kyau saiku yanka ta ruwa ya fito bayan ruwan ya fito saiku dinga goga ta a inda kurajen suka fito kokuma inda tabon yake.

Shima wannan ya kawar da kuraje fuska sosai ko tabon fuska kuma yana gyra fuska tayi kyau sosai.

Abin Lura:


Idan zakiyi amfani da Alobera ne to zakiji dan dacinta a makogwaranki saiki daure, Allah ya temaka kuma Don Allah idan harkin karanta to ki turwa yan uwa suma su amfana.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Mustapha Muhammad abba says

    Fimfus

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »