Takaitaccen Tarihin Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami.

0 2,386

Dakta Isah Ali Ibrahim Pantami, FNCS, FBCS, FIIM

Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, Malami a Computer Information System a Jami’ar Musulunci ta Madinah, kuma mashahurin malamin Islama ne. Zai kasance dan Najeriya na farko da ya fara koyarwa a cikin jami’ar Madinah sama da shekaru 63 da zama.

HAIHUWAR SA.


An haifi Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 20 ga watan Oktobar 1972 a garin Pantami dake Gombe a Najeriya. Yayi karatunsa na primary da secondary duk a Gombe.

KARATUNSA.


Dakta. Ya kammala Digirinsa na farko a bangaren Na’ura mai kwakwalwa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa Dake Bauchi (ATBU) a shekara ta 2002, haka zalika Dakta. ya kamala Digirinsa na biyu a bangaren Na’ura mai kwakwalwa a ATBU din a shekarar 2008. Sanan Dakta. ya tafi Jamiar United kingdom inda anan ya kammala Digirin digir-gir wato Phd a 2010.

FARA AIKINSA:


Dakta. Pantami Ya fara aiki a jami’ar ATBU, inda yake koyar da ‘Information Technology’ kafin daga bisani ya koma Jami’ar Musulunci dake Madinah

SAMUN MATSAYINSA A SIYASA:

Dakta in Office.

A shekarar 2016, Pantami ya ajiye koyarwa, inda a nan ne shugaba Muhammad Buhari ya nada shi ya zama shugaban hukumar ‘NITDA’ a ranar 26 ga watan Satumbar 2016.

LITATTAFAN DA DAKTA. YAWALLAFA.

Dakta. Ya wallafa litattafai da yawa a bangaren Addini, fasaha, siyasa da dai sauransu. Litattafan nasa sune kamar su:

  • The Negative impact of ICT on human health. Volume 2, no 2 Jomatech, 2010.
  • An analysis of e-learning in Nigerian and United Kingdom Universities. Volume 2, no 1, International Journal of Computer and Information Technology, India.
  • Information and Communication Technology, A Tool for Fraud Prevention and Detection. Volume 1, no 2 Jomatech 2008;
  • Data Recovery and Back up Disaster. Volume 2, no 1 Jomatech, 2008;
  • Analysis on the failure of Desktop and Laptop Hardware Components. Volume 2, no 1 Jomatech, 2008.

SAI WASU LITATTAFAN ADDININ ISLAM KAMAR HAKA:

  • Islam and Politics;
  • Synonimity or Dichotomy?;
  • The Essentials Of Marriage in Establishing An Ideal Family;
  • Month of The Qur’an & Its Virtues;
  • 63 Steps Of Performing an Acceptable Hajji & Its Spiritual and Moral Lessons.

LAMBOBIN YABON DA YASAMU:

Dakta Pantami ya samu lambobin yabo da yawa daga mutane da kungiyoyi da dama wadanda suka hada da wadan da suka fito daga

  • Shugaba Muhammad Buhari a ranar 29 ga Mayu, 2006;
  • kungiyar Muslim Corpers ta Nijeriya a ranar 19 ga Janairu, 2004,
  • Alhaji Ahmad Sani (Yariman Bakura) Babban Daraktan Gudanarwa na jihar Zamfara a ranar 4 ga Afrilu, 2006.
  • Kyautar ta nuna ƙoƙarin na koyar da ɗabi’a na gaskiya da sadaukarwa ga aikinsa. dadai sauran kyaututtuka da dama..
[review]
Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »