SHEIK KABIRU HARUNA GOMBE
An haifi Sheik Muhammad Kabiru Haruna Gombe, a garin Kuri a karamar hukumar Yamaltu Deba, a jihar Gombe.
Sheik yayi makarantar firamare a garin Gombe, a wata islamiyya ta Izala anan garinGombe. Sheik Kabiru Haruna Gombe ya samu haddar Al’qurani mai girma tare da gyara karatun sa a wajen maluma irin su:
- Sheik Zarma Gombe,
- Sheik Dr. Abdullahi Saleh Pakistan.
Sheik ya yi wasu karatunsa na ilimi a wajen maluma irin su:
- Sheik Usman IsahTaliyawa Gombe.
Sheik Kabiru Gombe ya zama Alaramma mai jan baki a Izala tun yana karami, kafin daga bisani ya juya zuwa mai wa’azi wanda a halin yanzu Karatuttukan sa ya zaga kasa daban daban.
Sheik Kabiru Gombe bai tsaya iya wa’azi ba, yana taba kasuwanci sannan babban manomine.
Sheik yana da mata hudu da yara da jikoki.