YADDA RIMAYEN ZAZZAU SUKA SAMO ASALIN SUNAYENSU

0 2,724

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zariya tana da wasu rimaye masu tarihi a cikin ganuwar garin. Idan aka ce zariya, ana nufin dukkan garin ciki da waje abin da ya shafi Sabon Gari, da Samaru da Basawa da Wusasa da Tudun wada, duk da gefen wadannan wurare duk zariya ake cewa. To, amma ainihin cikin garin zariya, shi ne inda ganuwar zariya ta zagaye garin, shi ne a Turance, Turawa suke kira “ZARIA CITY” Watau cikin garin zariya inda kofofin nan guda takwas suke hade da ita, watau Kofar Bai, Kofar Doka, Kofar Kibo, Kofar Jatau, Kofar Kuyan Bana, Kofar Gayan, Kofar Kona da Kofar Galadima.A cikin wannan gari na zariya akwai wasu rimaye guda shida (6) wadanda ake masu lakabi da irin abin da ke tare da su ko ta sanadin sunan mutum ko Dabba ko kuma dalilin wani abu da ke faruwa a wurin, wadannn Rimaye su ne, Rimin Tsiwa da Rimin Kwakwa, da Rimin Doko da Rimin Kambari da Rimin Danza da Rimin Bindiga.


 1. RIMIN TSIWA: Yana kan titin da za ka shiga cikin Unguwan Rimin Tsiwa a gefen Titi a kofar gidan Sarkin zazzau Muhammadu Aminu. Kuma ta can tsallake akwai tsohon gidan Ajiyan zazzau Alh. Sani Rimin Tsiwa. Ana kiran wannan rimi da wannan Suna a dalilin wasu tsuntsayen sukan ta kuka “TSIW TSIW”. A sakamakon wannan kukan ya sa aka sa ma wannan Rimin Tsiwa fiye da shekaru dari biyu da suka gabata. Kuma har yanzu sunan Unguwar kenan. Kuma a nan ne zuri’ar Malam Abdulkarimu, Sarkin zazzau , suka zauna, watau gidan sarautar Katsinawan Zazzau. Amma yanzu wannan Rimin ba ya nan an sare shi a lokacin Mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida, tsohon shugaban Kasar Nijeriya, saboda gyaran hanyar zariya. 2. RIMIN KWAKWA: Wannan Rimi na makwaftaka da Rimin Tsiwa kuma an sami wannan suna na Rimin Kwakwa a dalilin wasu tsuntsaye ne da Allah ya zaunar da su a wajen ko kuma kan Rimin. Su wadannan tsuntsaye suna da kama da Zalbe ko Shamuwa, amma ba shamuwa ba ce kuma ba zalbe ba ne. Kuma su ma suna da dogon baki da tsawon kafa.zariya.  A dalilin zamansu a wannan Rimi ya sa ake kiran Rimin ko wurin da Rimin kwakwa. Wannan Kwakwa na bayyana irin kukan da suke yi. Suna yin kuka kamar haka ” KWA, KWA, KWA.” Wannan shi ne dalilin kiran wannan wuri da sunan Rimin kwakwa kuma har yan zu ana kiran wurin haka.zariya.  Wannan Rimi yana a tsakanin hanyar zuwa gidan Sa’in Zazzau Umaru Jume. Yanzu wannan Rimi an sare shi lokaci guda da Rimin Tsiwa a lokacin Mulkin Janar Badamasi Babangida lokacin da ake gyaran hanyar cikin garin zariya.zariya. 3. RIMIN DOKO: Rimin Doko , yana Unguwar Kaura ne kuma ya sami wannan suna ne a dalilin wanban Zazzau Malam Marwa Doko, dan Sarkin zazzau Yamusa na gidan Sarautar Barebari na zazzau. Wannan Rimin yana kofar gidan Sarkin zazzau Malam Yamusa ne amma ana kiran gidan da GIDAN DOKO. Kuma nan ne Cibiyar gidan Sarautar Barebari na Zazzau. A Rimin Doko Wambai Doko yake zama a da. Kuma dalilin haka ne ya sa ake ce ma wurin Rimin Doko.
  .
 4. RIMIN KAMBARI: wannan Rimin yana kan titin Unguwar Kaura da hanyar da ta nufi Unguwar Nufawa ta titin kaura din., Rimin Kambari ya sami wannan suna ne a dalilin mutanen kambari da suka zauna zariya suna cinikayya da mutanen gari. Su Kambarawa mutanen wajen Yobe da Fika ne. A wannan gindin Rimi suke zama da shugabansu da ake kira Kambari, a dalilin haka ne wurin ya sami suna da kuma Rimin.
  .
 5. RIMIN BINDIGA: Rimin Bindiga shi ma makocin Rimin Kambari ne, Kuma shi yana da dadadden tarihi tun lokacin Mulkin Habe. Tanan Sarki ke bi idan zai fita gari ta Kofar Kuyambana ko Kofar Gayan daga Fadar Bono. Saboda haka idan ya fito nan za a dinga buga bindiga don a san Sarki ya fito yana tafe. Wani kaulin kuma ance, a nan ne wani Sarkin bindiga ya zauna tun a lokacin zuwan daular Mulkin Fulani a Zazzau. To, koma yaya ne dai, yanzu Rimin yana nan a kusa da gidan Wanban zazzau Usman dan Galadima Zubairu dan Sarkin zazzau Malam Yero na gidan Sarautar Barebari.
 6. RIMIN DANZA: Rimin Danza shi ma yana da dadadden tarihi, da ke da alaka da wani maharbi mai suna Danza kuma a dalilin sunansa ake kiran wurin Rimin Danza. Wannan Rimi masana tarihi sun ce ya sami sunansa ne dag wani gari da ake kira Danza cikin kasar Giwa, a hanyar Karaukarau zuwa Kadage. An ce sunan wani maharbi ne, da ya tashi daga garin ya dawo zariya. Akwai Rimi a kofar gidansa sai aka wayi gari Aljanu sun tunbuke Rimin sun biyo shi da shi zuwa Zariya.
  Wani kaulin kuma an ce sunan wani Sarki ne daga cikin sunayen Sarakunan Habe na Zazzau. Ana kiransa da Danzaki kuma shi ya kafa garin da ya tashi daga garin ya shigo zariya shi ne ya zauna a nan dalilin da ya sa ake ce wa wannan Rimi, Rimin Danza. To kodai yaya ne wannan Rimi yana nan a wani wuri. In ka fita ta hanyar zuwa kofar Kuyambana ta Durumin mai Garke zuwa Town School No. 1 sai ka bi ta jikin makaranta har zuwa Rimin Danza kusa da gidan wani sanannen Attajiri marigayi Alhaji Dahiru Kanti.

  Wannan shi ne takaitaccen bayani a kan tarihin wadannan Rimaye na zariya, kuma ko da ma zariya an san ta da Rimaye don har ana mata kirari da cewa ” RIMAYEN ZARIYA SUN FI ‘YAN MATAN ZARIYA ALKAWARI” kuma ana cewa ” RIMI ADON GARI A BIRNIN ZARIYA”
  Sauran Rimaye da suke wurare, yawancin su duk an shuka su ne ko a gona ko kan titi har ma a gida. Kamar yadda wani kauli na tarihi yace ” Rimayen da suka tashi daga Babban Dodo cikin garin zariya suka jeru har zuwa Tudun wadan zariya an shuka su ne a zamanin Sarkin zazzau Malam Aliyu Dan Sidi n gidan sarautar Mallawa, bisa umurni da shawarar Turawa a lokacin Mulkin Turawan Ingilishi. Haka kuma mutane kan zo daga wasu kasashe ru rayi irin wannan Rimi su je su shuka a kasarsu, sannan ana zuwa a sayi itacen wanda ya girma sare a sassaka Jirgin KwaleKwale don masu fito a ruwa.

  Kuma har ila yau ana amfani da ‘ya’yan wannan rimi inda ake cire audugar ciki a kada ta don yin Katifa da Matashi da Kahu da Huhu ko Kitifi. Yanzu haka akwai inda ake sarrafa wannan ‘ya’yan rimi a cikin garin zariya ana ce ma wurin Unguwar Kahu da kuma shugaban masu wannan sana’a yana da sarautar wakilin Khun zazzau.

Daga shafin Zazzau Ayau

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »