TARIHIN DR. LADI KWALI TA JIKIN NAIRA #20

0 4,144

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

WANNAN AHINE CIKAKEN TARIHIN HAJIYA DR.  LADI KWALI 

An haifi Ladi a wani kauye da ake kira Kwali, wanda a yanzu wannan kauye yana daga yanki a Abuja a shekara ta 5, 1925, wani tarihin nata kuma yana nuna cewa an haifeta ne a shekara ta 1920.

Ladi ta girma a cikin danginta ayayin da al’adar matan yankin suke kirar tukwane na kasa don dogaro da kawunan su.    

    Haka zalika Ladi Kwali ta koyi kerar tukwane ne a wurin kanwar mahaifiyar ta tun tana yar karama, kuma tasamu horar wa mai kyau a wajen kanwar mahafiyar tata, inda ta kware sosai wajen kirar tukwanen.    

Wannan dalilin na kwarewar tata yasanya da zarar ta hada tukwanan nata  kafin ranar kasuwa ta zagayo an sai da tukwanan.   

Ta sanadiyar wani baturen Ingila mai daukar hoton abubuwan ban mamaki mai suna Mikheal Cardew, Ladi Kwali tayi suna sosai a duniya a shekara ta alib 1950.    

    A shekara alib 1951, aka nada Mikheal Cardew a matsayin mai kula da Kera Tukwane a ma’aikatar kasuwanci da masana’antu inda ya kafa makarantar Kera tukwane a Abuja ya kuma jawo Ladi Kwali a matsayin mai horar da dalibai a shekarar alib 1952 zuwa alib 1967, wato sun shafe Shekaru 15 kenan sun koyar da tukwane  a wannan makarantar.  

Saboda kyawun tukwanan da Ladi Kwali ke kerawa da kuma sunan da sukayi gami da ingancin su yasa Sarkin Abuja na wannan lokacin Sulaiman Barau yasa takera masa tukwanan don ya kayata cikin fadarsa dasu.   

      Ladi Kwali da Michael Cardew sun tafi ziyayara kasar Ingila da Amuruka,  inda yake nuna  aitukanta kuma yaja hakulan mutane da dama a kasashen biyu.   

Shaharariyar A kera tukwane Ladi Kwali tasamu lambobin yabo da dama kamar haka. 

  • A shekarar January alib 1962 an Karrama Ladi Kwali da MBE, wato [Member of the Oder of the British Empire]. 
  • A shekara alib 1977 Jami’ar Ahmadu Bello dake zariya yabata digirin girmamawa na Dakta wato [Honorary Doctorate]. 
  • Gwabnatin tarayar Najeriya ta karramata da Lambar yabo mafi girma na Ilimi wato “Nigerian National Oder of Merit Award” 
  • A shekarar alib 1981, Ladi tasamu Lambar yabo ta OON, wato Office of the Oder in the Niger. 
  • An sanya hoton ta a bayan naira Ashirin na  kudin Najeriya, kuma itace mace ta farko da aka sanya hoton ta a jikin kudi a Najeriya. 
  • An canza sunan makarantar da takoyar da kera tukwane zuwa ta Abuja zuwa “Ladi Kwali Pottery”. 
  • An sanya sunanta a wani babban layi dake birnin Abuja mai suna “Ladi Kwali Street”. 

    Allahu-akhbar Ladi Kwali ta rasu ranar 12 ga watan ogas shekarar alib 1984, ta mutu tanada Shekaru 58 zuwa 59 a garin Mina dake Jihar Neja.     

Like and share Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »