AMFANIN BADO GA LAFIYAR JIKIN DAN ADAM

3 19,228

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 

 

 

 

 

YADDA DAN ADAM ZAI SARRAFA BADO DON AMFANIN KANSA DANA IYLINSA

 

 
Sautari wasu sukanga BADO kamar wani abin banza wasu kuma sukance Ana cinsa ne kawai saboda yinwa, kuma nasan cewa sunai masa Wannan fahimta ne sakamakon rashin sanin amfanin sa.
 
 
Masha Allah matukar kuna tare damu to zakuji amfanin sa yanzun nan. 
 
 
Zamu kasa shi gida uku
 
 
  • 1. Furen sa
  • 2. Saiwar sa
  • 3. Sai kwallon sa. 

 

 
 

 

FUREN BADO
 
 
 
Wannan fure na BADO yanan zaku ganshi kala biyu a wuri daya, fari-fari da kuma yalo-yalo. 
 
 
 
YADDA AKE AFANI DA FUREN BADON
 
To ita Wannan FUREN mai fari-fari da yalo-yalon nan saiku samota ku tattauna ta ku hadiya baki daya ko kuma ku shanyata ta bushe saiku dakata kudinga sanyawa a Shayi kunasha to yana magani kamar haka. 
 
 
  • Maganin Zafin Jiki. 
  • Maganin Radadin Jiki. 
  • Maganin zugin jiki. 
  • Maganin Shawara. 
  • Maganin Cutar Cizon Sauro {Maleria}. 

 

 

Harda Maganin zafin tafin Hannu Dana kafa.
Da duk wani nau’i na zafin jiki, sanan kuma shi furen bashi da wani daci ko bauri ko makamancin haka. 

 

SAIWAR BADO
 
Wannan saiwa ta bado itace ta Kama tundaga kan gayansa harzuwa karshensa da wani Dan kullutu to wannan dukka saiwar bado din kenan.  
 
 
YANDA AKE AMFANI DA SAIWAR BADON. 
 
Za’a samu mai kyau mai kuma tsafta sai a shanyashi yabushe sai adakashi sosai kamar gari kenan. Yana magani kamar haka:
 
GA MAZA
 
 
  • Yana Maganin Tsargiya {fitsarin jin}. 
  • Yana Maganin Ciwon Sanyi. 
  • Yana Maganin Kumburin Al’aura. 
  • Yana Maganin Kumburin Mara. 

 

 
 
 
GA MATA
 
 
  • Yana Maganin ga MATA masu zubar farin ruwa a gabansu. 
  • Ko ruwa mai nono-nono. 
  • Ko ruwa mai jini-jini. 

 

 
 

KWALLON BADO. 
 
 
 
 
Shi kallon bado yanan Wanda shi idan an fasa kwallon za’aga wani Abu kamar gero a cikinsa kuma yanan da wani fari-fari acikinsa. 
 
 
 
YADDA AKE AMFANIN DA KWALLON BADON. 
 
 
 
Zaka samu wannan kwallon bado din kabude cikinsa kadebe wannan yayan masu Kama da yayan gero, saika shanyasu Su bushe sai a dake makasu kamar gari saika nemi madara ta ruwa ko ta gari, ko kindur mo, ko ta shanu ko kowace irin madara. Yana magani kamar haka. 
 
 
 
  • Yana Maganin matsalolin hanji. 
  • Yana Maganin matsal olin mara. 
  • Yana Maganin matsalolin Sanyi. 

 

 

Tura Aiyukan Mu Zuwa daya daga cikin social media dake kasa Mungode

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. yaya t.kawuwa says

    godiya muke

  2. Ibrahim Adamu Gorondo says

    Allah ya saka da alheri
    Muna godiya

    1. alummarhausa says

      Amin Thuma Amin

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »