TARIHIN SHINKAFI TA JIHAR ZAMFARA

3 872

Get real time updates directly on you device, subscribe now.SHINKAFI

Hausa people 
WANNAN SHINE ASALIN TARIHIN YADDA KARAMAR HUKUMAR SHINKAFI TA KAFU
A  shekara ta 1802 kafin Jihadin Usman Danfodio, wani malamin Islama mai suna Mallan Muhammadu Zabo, daya daga cikin kakannin  daular Borno ya yi hijira daga yankin  gabas. Ya jagoranci makiyaya don bincike akan  koren wuri da yadace don yin kiwon dabbobi. 
Mallan Zabo ya kasance mai arziki matuka kuma ya ɗauki dabbobi da yawa, tsuntsaye, dawakai, matansa da kuma yara da wasu bayi. Har ila yau, ya bayyana cewa dukan tawagar  mutanene da suka zo tare da shi sun kasance daga cikin mutanen Barebari wanda suka fara zama  a garin da ke kusa da gari da ake kira  ‘Badarawa’. 
Daga baya tawagar  suka tsaya a kwarin kusa da kogin da suke kiransa “Tafkin Kaiwa” wanda yasanaya suka fara gineginene gidajensu na farko a wajen. 
Katsinawa masu cinikaiya sun kuma sami wuri mai  kyau donyin gidajensu a wurin.  don kwanciyar hankali, a wannan lokacin Gidan Dankwara Wasu rukuni na mutane da  suka fito  daga yankin garin Kwazare ta Jamhuriyar Nijar tare da jagoransu mai suna Adagwargo, wanda suke cikin kabilar Rahazawa, 
A wannan lokacin gidan  Sarkin Ruwa yana a yankin Barhazawa. Wannan makiyaya sunzo tare da garken shanunsu kuma sun haɗa su a kwarin inda suka sami mafaka da ruwa don ciyar da garken shanunsu. 
Kamar yadda suke hulɗa da haɗin kai tare da  Mutanen da suka  fara zama a wurin wato  Barebari, sakamakon hakan yasa yawan jama’ar  yankin ya zama dace ga masu ciniki da yawa, wadanda suke debt dare don yin kasuwanci.
Duk da haka wani rukuni daga cikin mafarauta waɗanda suka zo kusa da kwarin don neman dabbobin daji sun zauna a Yankin. Yankin  ya ci gaba kuma sun  zaune da  babban shugabasu, mai suna Mamman. 
Shugaban, mai mulkin Badarawa, na wannan lokaci  Magaji Bello, ya yanke shawarar sake Gurin zama a Gonar Mai Saje, (‘Yan Kukoki)  akwai ruwa da yawa.
 Mutanen sun zauna a yankin  kuma sun  fara noman shinkafa tare a kwarin Mai yawa, sabo  da damar da suk samu na samar da shinkafa  a yankin; Sai mutanen yankin suke kiran gurin Da suna ‘Shinkafi’ da hausa sunan  shinkafa.
Saboda rashin tsaro na zamanin, Magaji Bello ya gina  bango mai kauri da ake kira ( Ganuwa) wanda aka zagaye garin da ita. Zuriyar Magaji Bello ne yanzu Gidan Doka.
Zamantakewar  Al’umma  da tattalin arzuki na garin sun  sanya kasuwan cin kasa da kasa da ke jawo hankalin yan kasuwa  daga ko’ina cikin tarayya da sauran kasashen da ke makwabtaka kamar Jamhuriyar Nijar, Cameroon, Togo, Mali, da Jamhuriyar Benin, Chadi da Ghana. Akwai kuma akwai wadansu cibiyoyin sayar da kayan ƙanshin taba, wato Najerin Tobacco Company (NTC) da kuma Philp Morris Tobacco  Company ragowar sun hada da Cottage Industry. 
Saboda biyaya, addini da tattalin arziki da yin sulhu a tsakanin su ya janyo hankalin wasu ƙauyuka kamar irinsu Kamarawa, Shanawa, Badarawa, Isa da Sabon Birnin Gobir, kuma irin wannan ne ya zama Sarkin Gobir. 
Kawo yanzu dai Shinkafi taci gaba ta bangare daban-daban babban Asibiti,  Makarantu masu yawa, bankuna, wuri don cin abinci gami da babbar kasuwa data keci duk ranar Alhamis kasuwar kuwa tana tara dunbin Jama’a da suke zuwa dag kauyuka daban-daban . 
Shugabannin garin sun kasance da fara shugabanci tun daga shekara ta1835 har zuwa 2000, a lokacin da Babban Gwamna na Zamfara, Sen. Ahmed Sani (Yariman Bakura) ya kaddamar da shinkafi zuwa ga masarautar ( Emirate)   Sarkin Gabas na Shinkafi (Sarki na biyu). Shugabannin tun daga wancen lokacin zuwa yanzu sune kamar haka: – 
1. Magaji Mamman 1835 – 1845;
2. Magaji Bello 1845 – 1859;
3. Magaji Ibrahim I 1859 – 1874;
4. Magaji Bube 1874 – 1889;
5. Magaji Umaru 1889 – 1903;
6. Magaji Abdu 1903 – 1922;
7. Magaji Ahmadu 1922 – 1926;
8. Magaji Mainasara (Dango) 1926 – 1939;
9. Magaji Ahmadu Lamido 1939 – 1950;
10. Magaji Ibrahim II 1950 – 1990;
11. Magaji Mohammadu Moyi 1990 – 1994;
12. Magaji Mohammadu Makwashe 1995 – 2000;
13. Emir Mohammadu Makwashe 2000 – to

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

 1. Lawali Abdullahi Tsafe says

  Muna godiya ga wannan cibiya domin irin gudumuwar da take badawa a harshen Hausa, Allah kara daukaka

  1. admin says

   Amin Thuma Amin mungode

 2. Umar hamisu says

  Allah ka taimaki kasar hausa da hausawa

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »