Tarihin San’nar Kira A Kasar Hausa Kashi Na Biyu (2)

0 136

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

KAYAYYAKIN DA SANA’AR KIRA TAKE SAMARWA DON INGANTAWA DA TALLAFA WA RAYUWAR HAUSAWA

Kira dai kamar yadda muka sani, sana’a ce da ta jibanci sarrafa tama zuwa karfe daga nan kuma a samar da abubuwan tallafa wa rayuwar bil’adama, musamman Bahaushe.

 Haka kuma, sana’ace da take haifar da gudanar da wasu sana’o’i na zamantakewar Bahaushe ta yau da kullum. Daga cikin ireiren kayayyakin da makera suke kerawa domin tallafawa rayuwarBahaushe sun hadar da:

KAYAN YAKI:

Gabanin zuwan Turawa kasar Hausa, tarihi ya nuna cewa Hausawa da sauran kabilu na wannan shiyya suna zaune ne zama na dar-dar ko kuma mu ce zama irin na doya da manja, domin a kan samu yake-yake a tsakanin kabilu daban- daban ko tsakanin wannan gari da wancan gari domin mamaya da kara girman kasa ko kuma domin samun bayi. Ire-iren wannan yake-yake ana gudanar dasu ne da wasu makamai na musamman wadanda akasarin su makera ne suke kera su.

MAKAMAN SUN HADAR DA:

sulke da mashi da adda da wuka da tsitaka da gatari da takobi da sauran kayayyakin dawakan da ake yaki a kansu. Kamar irin su linzami da likkafa da garkuwa (karafuna ne da aka rufe fuskar doki dasu). 

Sabo da za muga cewa kira tana tallafa wa rayuwar Bahaushe domin samar da kayayyakin gudanar da yake-yakensu na wancanzamani. Duk da cewar yanzu an daina ire-iren wadaannan yake-yake har yanzu Hausawa na cin moriyar sana’ar kira domin samar da wasu nau’o’i na makamai kamar irin su barandami da lauje da bisalami da fate-faten takobi da sauran duk makami mai tasarifi da karfe.

Kayayyakin Gudanar Da Wasu Sana’o’i: Bayan samar da kayayya kin yake-yake da kayayyakin gudanar da wasu mashahuran sana’o’in Hausawa na gargajiya, kamar irin su noma da su da wanzanci da farauta da fawa da malanta da jima dasassaka da sauransu. Idan muka dauki noma zamu ga cewa akasarin kayayyakin gudanar da sana’ar ta noma tun daga gyaran amfanin gona har zuwa yankan amfanin gonar, duk Makera ne suke kera su kamar su magirbi da garma da kalmi da fatanya da dundurusu da lauje da wuka da sauransu.

Idan aka dauki su (kamun kifi) kugiya da sauran duk nau’in karfe da ake amfani da shi wajen kamun kifi da yankawa, hatta sarrafashi ko dai banda ko gashi ko suya ko makamancin hakan sai anyi amfani da kayayyakin da makera suka kera.

Haka abin ya kega sauran sana’o’in Hausawa na gargajiya kamar irin su wanzanci da farauta da malanta da fawa, duk askar da wanzami yake amfani da ita wajen gudanar da sana’ar sa ta wanzanci, za a tarar cewa makera ne suka kerata. Haka abun yake ga mafarauta duk makamin da mafarauci yake amfani da shi wajen gudanar da sana’ar sa ta farauta za a tarar makerane suka yi su. Misali, takobi da wuka da adda da barandami da tsitaka da Sauransu.

Idan aka dauki sana’ar jima, suna amfani da wuka da kartagi wajen aiwatar da sana’ar su, wadanda duk makerane suke kerasu. Haka abun yake ga masu sana’ar fawa, wukaken da jantadin da suke amfani da su duk makerane suka yi su. Haka abin yake ga masu sana’ar sassaka, duk nau’in kayayyakinsu akwai hannun Makera aciki, kamar su gizago da tsirya (karama ko babba) da gatari da mahuri da sauransu. Hatta malamai suna gudanar da sana’arsu da kayan kira, domin tauwadar da suke amfani da ita ana yin ta ne da kwan makera (tokar karfen kira), Domin samar da tauwada ta rubutu don ya yi rangadadau.

Saboda haka, kira gaskiya ne ta fi noman raggo kai! Har ma wanda ba raggo ba. Domin tana taimakawa wajen samar da kayayyakin gudanar da wasu sana’o’i na gargajiya domin samun abin masarufi daya jibinci ci da sha da sutura da muhalli.

MUHALLI– Muhalli dai, shi ne wata ‘yar farfajiya da mutum zai mallaka domin samun makwancinsa da na iyalansa. Bisa al’ada, a da can tarihi ya nuna cewa Hausawa suna zama ne a cikin kogon dutse. Wani kaulin kuma cewa yayi, su suke rarake dutsen su shiga ciki domin maganin ruwa da rana da abokan gaba. Da tafiya ta yi tafiya, suka fara yin amfani da itatuwa da karare da shifci da sauran nau’o’in itatuwa da ganyaye domin samar da muhalli. 

Haka kuma, lokaci ya zo da Hausawan suke samun dandankuwa da babarkiya ko burji domin yin tubalan da zasu gina muhallinsu. Wannan ya haifar da sanya abubuwa kamar su kofa da taga, wadanda duk makera ne suke kera su. Hatta abubuwa kamar su alharga da danta duk makera ne ke yin su. 

Saboda haka, a nan kira na tallafa wa rayuwar Bahaushe dangane da abin da ya shafi muhalli, domin Makera ne suke samar da kofofi da tagogi da sauran nau’o’in mukullai domin su zama kariya ga muhallin Hausawa.

Haka kuma abubuwa kamar su kwankwado domin tare gashin ka na mata da banbaro abin kadawa da baki domin samar da amo mai armashi duk makera ne suke samar da su.

YADDA AKE AIWATAR DA SANA’AR KIRA

Kamar yadda sauran nau’o’in sana’o’in Hausawa na gargajiya suke, dangane da yadda ake gudanar da kowace sana’a, Kira ma haka abin yake, wato ‘ya’ya da jikoki sukan bi iyaye da kakanni wajen aiwatar da sana’ar Kira, domin su taya iyayen nasu gudanar da wannan sana’a.

Tun farko, yaro yakan fara koyon sana’ar ne daga zuga ko hura wuta da zugazugi. Daga nan duk zai ga yadda ake gudanar da ita (sana’ar kira) da kuma yadda ake amfani da duk sauran nau’o’in kayayyakin aiwatar da sana’ar. Ana nan har zai faradan karambani irin na yara wajen wasa da kayayyakin, a hankali ana kwabarsa, ana kuma gyara masa har ya koya.

Kira itace tsantsar kimiyya da fasaha irin ta Bahaushe. Domin sana’a ce da ake tafiya mai nisa domin samo sinadarin yin ta (tama). Daga nan, za’a zo ayi ta bai wa tamar nan wuta da zugazugi har sai ta nade, kuma, kumfa ta rufe ta. Daga nan, za’a bambare kumfar, a sami tsurar karfen.

Wannan karfe shi ne za’a guggutsira shi da kurfi, sannan a bashi wuta, a sa hantsaki ko awartaki, a dauko shi, a dora kan uwar makera, a doddoke shi, sannan a lauya shi irin yadda ake so domin samar da ire-iren abubuwan da ake samarwa ta hanyar wannan sana’a domin tallafawa rayuwar Bahaushe ta yau da kullum. 

DAGA:

Tsangayar Daukaka Harshen Hausa Da Al’adu Da Kuma Adabi

MANAZARTA

Musa H. Modibbo, (1979): “Ciniki da Sana’o’I a Kasar Hausa”. General Editor; Ibrahim Yaro Yahya. Thomas Nelson Publishers.

Muhammad Abdu Durumin-iya (2006) “Tasirin Kimiyya da Kare- karen Zamani A kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya”. Kabs Print Service (NIG).

Aminu M.S (1993) “Faduwar Sana’o’in Gargajiya a Zamanance”, Kundin Binciken na neman Digiri na farko.

Tattaunawa da Mallam Umaru Makeri da ke unguwar Yamadawa, ranar Talata 16th-09-2014, da misalign karfe 5:30

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »