Amfanin Bawon Abarba Ga Lafiyar Jiki.

0 241

Daga yanzu mu daina zubar da bawon ABARBA saboda yana da matukar amfani game da lafiyarmu fiye da yadda muke tunani. Ga kadan daga cikin aikinsa nan:

1- Yana daidaita matsalar hawan jini. Da YARDAR ALLAH.

2- Yana sanya kwarin kashi da kwarin hakori/haure. Da YARDAR ALLAH.

3- Yana Magance matsalar sanyi da tari. Da YARDAR ALLAH.

4-Yana taimakawa wajan kawar da matsalar cutar Cancer. Da YARDAR ALLAH

5- Yana Karawa mace Ni’ima kuma yana karawa namiji kuzari. Da YARDAR ALLAH.

Yadda za ka hada shi shine kamar haka:

Za ka samo bawon abarba da Lemon tsami babba guda 1 da Garin Tumeric , sai ka yayyanka Bawon abarba din da kuma lemon tsamin kanana-kanana sai ka zuba a cikin wata tukunya, sai ka sanya garin Tumeric cokali daya a ciki sai a zuba ruwa kamar kofi daya da rabi sai a tafasa su tsawon mintuna 10 zuwa 15, arika sha da dumi kamar Tea safe da yamma. In Sha ALLAHu za kuga abin al’ajabi game da jikin ku.

Idan matsalar Infertility ( both ga maza da mata) ce kuma wacce take kawo jinkirin haihuwa a wasu lokutan sai a samo wannan hadin, Bawon abarba, lemon tsami da kuma Ganyen doddoya/Kafi Amarya ( Scent Leaf/Raihaan) sai a yayyanka su a tafasa a sanya ruwa kamar litre 1 a ciki sai a tafasa su tsawon mintuna 30, sai a rika sha safe kofi 1 da dare na kofi 1.

In Sha ALLAHu wannan hadin zai wankewa mace mahaifa daga abubuwan da suke hana a shuka kwayoyin halitta a cikin mahaifar kuma idan har ta dage da amfani da shi In har matsalar Infertility ce ke damunta ( bayan ta je wajan masana sun bata shawarwari da kuma wasu ƙarin abubuwa to da Yardar ALLAH za ta samu lafiya idan har Allah ya yi raba da rabin haihuwa a duniya.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »