Amfanin Ganyen Plantain Ga Lafiyar Jiki.

0 196

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai fama da ciwon : Zuciya, hawan jini da kuma cutar Prostate cancer ko Prostate enlergment ( Cuta ce wacce take kama mara ko mafitsarar mutum, tayadda za rika yin fitsari da kyar ba yadda yakamata ba sakamakon toshewar mafitsarar) wanda idan har mutum bai dau matakin da yakamata akanta tun farko ba za ta iya haifar masa da matsala wacce za ta fi karfin tunaninsa. Allah ya kyauta.

A samo ganyen Bishiyar PLANTAIN iya gwargwado busasshen wanda ya bushe a jikinta, sai a tsaftace shi kuma a tafasa shi har na tsawon mintuna 20 , sai a sauke shi a sanya zuma a ciki sai a rika shan kofi daya safe da dare.

In sha ALLAHu za kuga abin mamaki domin za ku rika fitsarar da duk wata matsala ne da ke cikin marar domin yana magance matsalar “Bladder infection” kuma ta bude duk inda ya toshe a mafitsara ko a marar mutum da DA YARDAR ALLAH.

Idan mutum yana shan wannan hadin kai akai kuma yana tauna danyen ganyen PLANTAIN din, hakan yana karawa zuciya karfi da lafiya cikin iko DA YARDAR ALLAH.

ABIN LURA.

Ganyen PLANTAIN nake nufi ba Ganyen BANANA ba, domin suna yanayi sosai ko ince ma duk kusan kalar bishiyunsu daya ne, amma za kuga ya’yan ne suke bambanta, ita BANANA yayanta kanana ne basu kai na PLANTAIN girma ba. ALLAHu A’alam.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »