Yana Da Matukar Amfani Ga Masu Fama Da Ciwon Suga (Diabetics)

0 561

Ga abubuwan da za ka samo nan:

1- Kubewa guda 2.
2- Cucumber rabi 1/2.
3- Lemon tsami rabi 1/2.
4-Garin Zogale cokali daya.
5- Ruwa kofi daya.

Sai a yayyanka duk abubuwan da na lissafa din nan gutsi-gutsi, sai a sanya su a blender a zuba ruwa kofi daya sai a markada su, bayan an tace sai a zuba garin zogalen cokali daya a ciki, sai a juya su sosai idan aka tabbatar ya garwayu sai a shanye.

Kullum arika yin haka idan akayi na tsawon kwana uku ko sati daya ana yi, sai a koma asibti a duba jikin, in Sha ALLAH za a ga sauyi kwarai da gaske da YARDAR ALLAH.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »