Wasu Daga Cikin Nau’o’in Sihiri Da Kanyi Tasiri A Jikin Dan Adam.

0 225

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Akwai wasu nau’ukan SIHIRI da suke shiga cikin jikin mutane kuma suyi tasiri kai tsaye ( amma musani cewa: Babu abinda wani zai yiwa wani na amfani ko na cutarwa yayi tasiri a jikinsa duk sai da IZININ ALLAH). sune kamar haka:

1- SIHIR Al- MA’AKUL da MASHRUB: Sihrin da ake sanyawa mutum a cikin abinci ko abinsha. Shiyasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu Addu’ar cin abinci da shan abinsha akalla muce: “BISMILLAH” a lokacin da za muci abinci ko shan abinsha ( Duk wanda yake yin Addu’ar nan to In Sha Allahu Allah zai kare shi daga Sharrin duk wani sihirin da aka sanya a cikin abincin ko abinshan.)

2- SIHIRI ALMARSHUSH : Sihirin Barbade, wanda ake barbadawa mutum a tufafi ko kan gado ko shimfida, ko a kofar gida ko ta daki, ko cikin daki ko wuraren da akasan wanda za ayiwa Sihirin yana wucewa ta wurin.

Shi yasa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu Addu’ar sanya tufafi, kakkabe wurin kwnaciyar barci kafin mu kwanta, Addu’ar shiga da fita daga gida. ( In sha ALLAHu duk mai bin waɗan nan ka’idojin Allah zai kare shi daga Sharrin duk wani Sihirin da aka barbada a tufafi ko kan hanya ko kan gado da sauransu.)

3- SIHIR ALMASHMUM : Sihirin da ake sanyawa a turare na ruwa ko na wuta domin wanda aka yiwa sihirin ya shaka kamshin ko hayakin turaren. ( Shi yasa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koya mana zama cikin Azkaar safiya da maraice ba dare ba rana da yawaita sauraron Alqur’ani da karatunsa. In Sha ALLAHu Allah yana baiwa masu neman kariyarSA da taimakonSA kariya kuma ya tsare su daga dukkanin sharrin halittunSA.

Wadannan nau’ukan SIHIRIN duk sun HARAMTA daga wanda ake yi domin cutar da wani har wadanda ake yi domin karkato da zuciyar wani ko a mallake shi sai abinda akace wannan Addinin Musulunci ya haramta haka.

Ya zama wajibi masu yi su daina tun kafin suje su hadu da ALLAH ya hukunta su, saboda Allah ya Haramta kuma ya tsinewa duk wani matsafi da wadanda ke hulda da matsafa. Tun a nan duniya Allah yake nuna musu Ishara wajan lalacewar Sihirin ko kaikayi yakoma kan mashekiya ko Allah yasa Mutum ya wulakanta ya tagayyare yarasa me ke yi masa dadi a zaman duniya. Sai a kula da kyau… Allah yakara tsare mana imaninmu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »