Yadda Ciki Yake Shiga Mace Da Yadda Za’a Kula Dashi Har Zuwa Matakin Haihuwa

0 637

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ma’anar Juna Biyu

A takaice shi ne a samu mace tana dauke da cikin jariri shi ne juna biyu.

Yadda cikin yake shiga shi ne:-

Bayan kwana goma ko makamancin haka bayan da mace ta duba al’ada kwai yagama nuna zai bi hanyar kwai.

Idan mace ta hadu da na miji kwan namiji diyawa za su samu shiga hanyar makwancin kwai wasu har cikin makwancin kwan suna shiga.

Sai kwan na miji daya ya shiga kwan mace, a wannan lokocin sabon rai zai soma. Sauran kwan namiji dukka za su mutu. Kwan mace wanda ya zama sabon rai yanzu zai ci gaba zuwa makwancin yaro.

MASANA KIWON LAFIYA SUN KASA CIKI ZANGO UKU:-

1- Zango na farko shi ne (wata ukun farko)

2- Zango na biyu shi ne (wata ukun tsakiya)

3- Zango na uku shi ne (watanni uku da sati 2 na karshe)

1- A Zango na farko:- A watannin farko dayawa daga cikin mata basa iya fahimtar canje-canje da ke faruwa da su, musamman ma ga wadanda basu taba haihuwa ba.

Yana da matukar mahimmanci mata masu ɗauke da juna biyu su san alamomi da canje canje da za su fuskanta yayin watannin farko.

Daga ciki akwai:-

1- Ketare wata

2- Tashin zuciya

3- Gajiya

4- Amai

5- Nonuwa suna kara girma.

6- Zazzabin safe

7- Yawan fitsari

8- Yawan kwadayi

9- Kyeman wassu Abincin

10- Yawan kasala da mutuwar jiki.

2- Zango na biyu:-Wata ukun tsakiya a wannan lokaci masu juna biyu sunfi samun natsuwa da kwanciyar hankali sabida da yawa daga cikin alamomi da matsalolin da suke fuskanta a watannin farko kamar su tashin zuciya da amai da sauransu sun ragu.

Sannan kuma har ila yau ciki be girman da zai hanasu walwala ba.

Canje canje da za’a gani a wannan lokocin sun hada da:-

1- Girman ciki.

2- Canjin Launin fata.

3- Yawan Jiri.

4- Yawan Mura.

5- Ciwon Mara.

6- Kullewar Mara.

7- Girman nono.

8- Fitar da farin ruwa daga al’aura.

9- Ciwon kafa.

10- Ciwon kai.

3- Zango na uku:- watanni ukun karshe yayin da abin da ke ciki ya kawo wannan watanni, yanayin motsinsa a ciki ze karu.

Daga cikin matsalolin da masu juna biyu suke fuskanta awannan lokaci sun hada da:-

1- Ciwon mara kamar nakuda.

2- Ciwon Baya.

3- Rike Numfashi.

4- Zafin Zuciya.

5- Kumburin jijiyoyin kafa.

6- Yawan Fitsari.

7- Wahalar fitar da bahaya.

8- Basir.

A DUNKULE DAGA SHIGAR CIKI ZUWA HAIHUWA ME MACE MAI CIKI TAKE BUKATA:-

1- Mata masu ciki da zaran ciki ya shiga har zuwa ranar haihuwa su dage cin kayan marmari da ganyayyaki sosai, kamar sau biyar a rana.

Gasu kamar haka:-

 • Salat.
 • kabeji.
 • Alayyahu.
 • karas.
 • Lemo.
 • kankana.
 • Apple da sauransu.

2- Tun a watanni uku na farko za ta fara amfani da kwayar Folic Acid domin baya ga karin jini tana da amfani sosai.

Domin tana taimakawa wajen kariya ga haihuwar yaro mai nakasa a jiki.

3- Da zarar an fita a watanni uku na farko sam kada a manta da zuwa awun juna biyu wato (ANTENATAL).

4- Shan magani barkatai ba tare da likita ya rubuta ke mai ciki ba naki ba ne, ko paracetamol da muka raina tana da illa.

5- Su kuma ci abinci mai dauke da sinadarin Protein wato mai gina jiki da suka hada:-

 • Nama.
 • Kifi.
 • Kwai.
 • Wake da sauran su.

6- Haka ma abinci mai dauke da sinadarin Calcium kamar su madara da kindirmo ko yogurt suna da amfani matuka.

7- Yana da kyau kuma su ci kifi mai maiko kamar su mackerel da sardines, amma su guji cin kifayen da suka hada da shark da swordfish.

8- Sannan yana da kyau su guji cin wasu nau’in cukwi da suka hada da Brie da Camembert da Gorgonzola da kuma Roquefort suna zubar da ciki.

9- Abu na karshe shi ne ayi kokorin a haihu a asibiti, domin hatsarin dake tattare da haihuwar gida.

Anan zamu tsaya InshaAllah

SHIFA TRADITIONAL MEDICINE

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »