Muyiwa Junan Mu Riga-Kafi Don Samun Tsaro Da Kariyar Allah.

0 131

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Matukar kuna son samun tsaro, kariya da kuma kiyayewar Allah mai kowa da komai daga dukkanin sharrin halittunSA, to karku zamo cikin masu aikata wadan nan abubuwan:

1- Rashin karatu da sauraron Alqur’ani a ko da yaushe

2- Rashin cewa: “BISMILLAH” a lokacin da mutum zai cire ko zai sauya tufafi.

3- Rashin yin Addu’a yayin shiga ban-daki (toilet).

4- Sauraron kade-kade da yin rawa a gaban madubi (Mirror).

5- Fita daga gida ba tare da yin Addu’a ba kamar kace: “BISMILLAH TAWAKKALTU ALALLAHI WALAA HAULA WALAA QUWWATA ILLA BILLAH.”

6- Zuwa ko shiga kasuwanni haka kurum ba tare da wata bukatar siye ko siyarwa ko makamantan hakan ba.

7- Bayyana kwalliya a bainar jama’a ko a waje ko wajan taron bukukuwa.

8- Rashin yin Azkaar din safiya da maraice da lokacin kwanciya bacci.

9- Rashin kwanciya ba tare da alwala ba.

10- Zuwa wajan bokaye ko hulda da masu zuwa wajan Bokaye.

Wadannan abubuwan ya zama dole mu kaurace musu daga mazan har matan, masu aure da marasa aure, domin: Sihiri, Hassada, Kambun-baka ko Kambun-Ido da kuma duk wani nau’ikan sharri na shedanun Aljanu da na mutane tsaf za su iya samun damar shigar mutum cikin sauki.

Idan kana cikin masu aikata hakan, to duk abinda yasameka karka zargi kowa sai kanka.

Allah yakara tsare mana imaninmu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »