Wasu Abubuwa Da Ma’aurata Ya Kamata Su Kula A Kansu Sosai

0 212

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Da zarar ma’aurata suna tsintar kansu cikin yawan samun sabani da mushkiloli a zamantakewar aurensu ba tare da wani dalili ba, da kuma yadda mace ke neman saki a wurin mijinta ba tare da wani dalili ba (kawai ita dai tana jin ba ta son zaman gidan).

Ko mace ta rika jin dadin zama da taji mijinta ya isheta taji ba ta kaunarsa ko ba taji kamar kar yadawo gidan, haka kurum ba tare da wani dalili ba, ko shi mijin yarika jin son rabuwa da matarshi ba tare da wani dalili ba.

Da zarar ma’aurata na fuskantar haka to ya kamata su rika kai zuciyarsu nesa kuma su dukufa wajen yawaita ibada, Addu’a da sadaqa, da kuma yawaita karanta Suratul Baqara da sauraronta, da yawaita karanta Suratul Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Falaqi da Nasi akai akai, da riko ko amfani da sabubban da suke warware Sihiri wadanda basu sabawa Shari’a ko tafarkin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ba.

Saboda Yawancin irin wannan matsalolin ba sa rasa nasaba ne da SIHIRI ko makamantanshi wanda Bokaye ko Shaidanu ko makiya ke kullawa domin raba tsakanin ma’aurata.

Allah yakara tsare mana imaninmu.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »