Ahmad Ali Nuhu yaro ne a wajen Jarimin fina-finan Hausa Kannywood wato Ali Nuhu wanda ake masa lakabi da Sarki a masana’antar tasu.
A tattaunawan da manema labarai sukai dashi akan Fara film dinsa ya bayyana cewa da wayansa fim daya fara shine ‘Charbin kwai” wanda kuma baifi scene guda 10 ba wanda yayi a cikin shirin, a wannan lokacin ne ya fara yin fim kuma ya fara sanin yadda harkar take, duk da ya bayyana cewa a yanzu yanaso ya dakata da fim saboda akwai Burinasa a rayuwa wanda yakeso ya cimma wato “Football” ( Kwallon Kafa ) wanda a inda yake zaune yana buga kwallo a wani Team sannan a makarantar su na ‘Yan Dutse College nan ma yana buga kwallo, sannan yana buga numba 10 ne a bayan rigar sa.
ABUBUWAN DA SUKE SANYASHI FARIN CIKI
haka zalika ya bayyana abubuwa wadan da suke sayan shi farin ciki suna da yawa, amma daga ciki yace idan sunayin was an kwallo da wata kungiyar suka zura kwallo a raga hakan na sashi murna ko kuma yayi passing a exam nashi hakan na matukar yimai dadi.
ABINDA YAKE BATA RANSA
sannan ya bayyana abin da yake batamai rai inda yace yadda ake zagin mahaifinsa hakan na matukar yimai ciwo amma hakanan yake sharewa amma a zahiri hakan na yimasa ciwo sosai.
ABIN DA KE BASHI WAHALA WAJEN YI
A cikin fina-finan da yayi ya bayyana film din Dan “Almajiri” a Matsayin fim din da yafishan wahala a cikin sa saboda akwai abubuwan dabai saba yin suba amma kuma sai dayayi,
FILM DIN DA YAFI JIN DADIN SA
Sanan ya bayyana Fim din “Uba da Da” fim din daya yafi jin dadinsa saboda bai jima da yawa ba kuma babu scene masu wahala a cikin sa, hakan yasa film din bai bashi wuyar yiba
ABIN DA YAFI MUHIMMANCI A WAJEN SA
Abinda yafi komai muhimmanci a wajen sa a rayuwa ya bayyana cewa Ahalinsa sune abu mafi muhimmanci a rayuwar sa.