Tarihin Ado Ahmad Gidan Dabino

0 262

TARIHIN ADO AHMAD GIDAN DABINO GWABNAN ALFAWA A KWANA CASIN.

Ado Ahmad Gidan Dabino M.O.N An haifeshi a ranar 01 ga watan Janairu shekarar alib 1964 a wani gari da ake kira Dan Bagina a karamar hukumar Dawkin Kudu amma an yayeshi a zangon Bare-Bari cikin Birnin Kano yayi karatunsa na Allo da Islamiyya duk a garin Kano duk da bai sami damar yin karatun Boko yana karami ba sai lokacin da yake da shekara 20 ne ya kai kansa Makarantar Ilimin manya ta Masallaci (Adult evening classes), Makarantar da Marigayi Barden Madakin Kano Alh. Garba Baban Ladi yake jagoranta, anan yayi Primary ta shekara 2.

Daganan ya tafi GSS Warure Evening Classes itama wanda akeyin Darasi da daddare kuma Makarantace da take Karkashin Hukumar yada Ilimin manya ta Jihar Kano, anan yayi shekara 4 yayi Karatunsa na karamar Sakandire da babbar Sakandire a shekarar alib 1986 – 1990.

Kuma ya sami dama yaje jami’ar Bayero inda ya karanta Aikin jarida fannin kwararru, (Professional Diploma in Mass Communication) a shekarar alib 2005 – 2006 kuma yayi course na karatun Makafi (Special Education) wanda suke koya domin su koyar da makafi.

FARA HARKAR FIM DINSA.
A Tattaunawan sa da manema labarai ya bayyana cewa kusan lokaci guda ya fara Rubutun Littafai da harkan film (Wasan Kwaikwayo),a shekarar alib 1984 yafara yin wasan kwaikwayo na Da6e a Kungiyar “Gyaranya Drama” sannan a shekarar alif 1984 ya fara Rubuta gajerun labarai wanda yake aikama shashin Hausa na Muryan Jama’a Dake Jamus, suna biya a lokacin, Sannan ya bayyana harkan Rubutun a matsayin abinda yafi yi sosai da film inda yake misalta shi da kusan kashi 90%.

RUBUTUNSA NA FARKO
Ya bayyana Littafin Hattara masoya a matsayin littafin daya fara Rubutawa a shekarar alib 1989 amma bai bugashi ba a lokacin saboda masu magana suna cewa tsalle daya ke jefa mutum Rijiya, yace a lokacinnan idan an fidda Littafin nan zaiyi ta rigima da mata bazasu soshi komar “Inda so da Kauna” ba don haka sai yafara buga INDA SO DA KAUNA littafin yaba kowa hakkin sa Maza da Mata ya fidda shi a shekarar alif 1990.

Sai dai yace nan gaba baya tunanin zaiyi Rubutu kamar yadda yayi a baya domin a baya lokacin ba iyali sannan kuma da saukin gwagwarmayar Rayuwa a yanzu kuma ga Shekaru ga Al’amura na yau da kullum sannnan Rubutun da yayi a baya bazai iya yinsa yanzu ba amma a cikin dukkan Rubutunsa bai taba Rubuta abin da yayi dana sanin Rubutashi ba, kuma dukkan abinda ya rubuta zai iya tsayawa ya kareshi a wajen dukkan mai kalubalanta har yau har gobe.

FIM DINSA NA FARKO
Ya bayyana film din “Inda so da Kauna” a matsayin film dinsa na farko sannan yace wannan film littafin sane ganin karbuwar sa yayi tunanin yin Bidiyon sa domina lokacin Littafin ya zama abinda ake kira a turance wato Best Selling Hausa Novel ma’ana littafin da akafi sayansa sosai a kasuwanni fannin Kirkirarrun Labarai wanda ya saida sama da copy 300,000 a iya kididdigan da yayi kuma an fassara Littafin zuwa harshen turanci wato soul of my heart, wannan shaharar da littafin yayi yasa mutane sukace yakamata a juyashi zuwa Bidiyo, kuma ya juyashi a shekarar alif 1994 – 1996 ya fiddashi kuma ya saka duk Najeriya a nuna shi a (Gidajen Kallo).

YAWAN FINA-FINAN SA
Ado Ahmad ya bayyana cewa yayi fina finai na kallo guda sha takwas 18 saboda mafi yawa a da can baya fitowa a fina-finai wajen ma’ana wanda bana kamfaninsa ba duk yawancin finanan kamfanin sa ne, kuma sau 1 yataba fitowa a matsayin Jarumi a film dinsa mai suna “inda da kauna” amma duk sauran yafi fitowa ta musamman wato Special Affaires a fitowa Daya, Biyu , zuwa Uku. Amma yafi tsayawa a Producer, ko Durector ko kuma marubuci a cikin finafinan kamfanin nasa.

Amma daga baya bayan ya kusan shekara goma sha baiyi film ba sai aka dawo dashi da karfi da yaji a shekarar 2016 sandiyyar wani film mai suna “Juyin Sarauta” wanda Hajiya Balaraba Yakubu” Tayi.

LITTAFAN DAYA RUBUTA
Ya bayyana Littafan daya Rubuta zasu kai 15 wadanda ya fiddasu kuma ananan ana karantasu wasu a Jami’oi wasu a Kwalejin Ilimin, wasu kuma a kasuwanni banda wadan da bai riga ya fiddasu ba tukunna.

Daga Bakin Mai Ita BBCHAUSA.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »