SANADIN SO KASHI NA SHIDA
Fateema taci gabada cewa, Ba karamar barazana na fuskanta ba Saboda na san ba abu ne mai yiwuwa ba nayi soyayya da kai alhalin da aure a kaina, Wannan ya sa na shiga tunanin mafita, daga baya na yanke shawarar na boye maka ina da aure.
Idan har ba yaudarata kike yi ba maganar da kika fada gaskiya ne ya akayi Kwamanda ya san muna tare?
Akasi aka samu nayi rashin lafiya ne mai tsanani wacce ta kaini ga kwanciya asibiti, bana raba daya biyu WhatsApp dina ya shiga yai min bincike anan yaga Chat dina da kai, kuma har kaje gidan ka dawo ban san an yi ba ina Asibiti.
To ya aka yi kika sani? Bayan kin ce ba ki gidan. Shi ne ya sanar dani bayan naji sauki. To wane mataki ya dauka a kanki? Hmm! Kudancy kenan, idan akwai abinda Kwamanda ya tsana a rayuwarsa to bacin raina ne, shi yasa duk abinda nayi bayamin fada bare har ya dau wani mataki a kaina. To yanzu me kika zo yi wurina? Kuma me.kike so in yi maki?
Hakuri na zo baka, a kan abinda yai maka, sannan kuma naga kayi blocking dina a facebook da WhatsApp shi ne na so jin dalilin hakan? Zancen Hakuri nayi, zancen Blocking kuma saboda ba zai yiwu in ci gaba da soyyaya da matar aure ba, a matan auren ma kuma matar soja. Sojan ma kwamanda Ba soyayya zamu ci gaba da yi ba Kudancy, kawai gaisawa zamu rika yi kuma ka ci gaba da turomin Labarai.
Ta fada tana yi min wani kallo, wanda ni a ganina na yaudara ne. Ba zai yiwu ba Fateema, zai fi kyau ki kama
gabanki kar ki sake jefani a wata musibar. Ka gasgatani Kudancy nayi maka Alkawarin babu abinda zai sameka wancan karon ma akasi aka samu. Tace dani Na fada maki fa ba zai yiwu ba, ki sani ko wannan hirar da muke yanzu zunubi ne muke kwasa saboda haka kawai ki kyaleni kar ki sani fadawa cikin fushin ubangiji. Ba irin magiyar da bata yi ba, amma naki
amincewa, dole ta hakura.
Da zata tafi kudi ta dauko daga jakarta wadanda ba xan iya cewa ga adadinsu ba, amma a kiyasin da nayi kudade ne masu tarin yawa ta ajiye a kan telata, Na meye? Na tambayeta. Baka nayi, na san ba zaka rasa ‘yan hidindimu a gabanka ba. Tace dani tana kokarin fita.
Kuma sai na ce dake bani da kudin da zan yi hidindimun nawa ko? Kar ki mayar dani wata haja mana, wacce zaki rika saye da kudi a duk lokacin da kika ga dama. Na fada a fusace.
Kayi hakuri ba nufi na ba kenan, gani nayi ba komai ba ne don na baka kyauta, amma tunda kayi min wata fassara, shi kenan ba zan kara ba. Zai fi kyau hakan, nace da ita ina kokarin mika mata kudin. Na dauka ta hakura kamar yanda ta nuna ashe tana kasa tana dabo, gwara ma a ce na amince da bukatarta a kan abinda ya biyo baya HAKAN SHINE BABBAN KUSKURENA DAYAFI NABAYA..
Hankalina ba karamar kwanciya yayi ba ganin cewa na yadda kwallon manguro zan huta da kuda. Bayan kamar kwana biyar da zuwan fateema shagon da nake dinki.
Da sassafe ina kwance dakina dake kofar gidanmu na ji kanina aliyu yana kwankwasamin kofa, koda na bude yake shaidamin wai nayi bakuwa tana nan kofar gida tana jira.
Kaina ba karamar daurewa yayi ba jin cewa wata ta zo nemana har gida domin kuwa wannan shi ne karo na farko da mace ta taba zuwa nemana a gida.
Duk matan da nake yi wa dinki sai dai su zo nemana a shago kuma ko basu sameni ba Aminu wanda muke dinki tare zai kirani a waya in zo. Cike da mamaki na fito daga dakin na nufi kofar gidanmu, tun daga nesa na hango mota tsugunne a kofar gidan, bana rabdaya biyu motar fateema’ce gabana ya badassKamar in juya sai dai na daure na isa. Ta bude ko sashen mai tuki ta zuro kafafunta waje sanye cikin jan material rike da waya kirar Sony Ericson Xperia tana chating. Fateema ce.
Murmushi ta jefeni da shi yayin da ni kumna daure fuska tare da jeho mata tambaya. Me kika zo yi a gidanmu?
Wurinka na zo Kudancy ta fada tana kokarin mikewa tsaye.
Haba! Fateema yanzu kina ganin ya dace a
matsayinki na matar aure ki rika zuwa
wajena, kuma baki tunanin zuwanki gidanmu zai iya haifarmin da matsala wajen iyayena? kuma kin san mijinki yai min tsakani da ke.
Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda
gaba daya na gama tsinkewa da al’amarinta…
Ku biyo ni a Kashi n 7 kuga yadda zatakaya sakanina da kwamanda.
Ab Kudancy