Sanadin So ( Kashi na 5 Hausa Novel )

0 86

SANADIN SO KASHI NA BIYAR.

zamu ci gaba daga inda tazo shagona

Kamshin turaren da ya gauraye madaidai cin shagon shi ya kara tabbatarmin da shigowarta ciki, gabana sai tsananta bugawa yake kara yi, tunanin masifar da zan sake shiga ya sani tsurewa.

Sallamar da tayi min ce ta sa ba shiri na daidaita kaina nayi kokarin boye fargabar da ke kokarin bayyana a fuskata. Sannunka Tela, tace dani. Yauwa sannunki, na amsa mata. Dinki nake so kayimin, ta gabatarmin da bukatarta Ga shi kuwa kin zo a makare. Na fada cikin gatse. Murmushi tayi sannan tace wane irin makare sai kace wacce ta kawo dinki daren Sallah kuma tace yanzu take son a dinke mata. Ba wannan makarar kika yi ba Hajiya, ina nufin kin zo a lokacin da na daina yi wa mata dinki, na fadi haka ne saboda tsayuwarta cikin shagon ta fara gundirata kuma a koda yaushe gani nake Kwamanda zai iya fadowa cikin shagon. Maganar da na fada maimakon tayi sanadiyar barinta shagon, ga mamakina sai gani nayi ta nemi kujera ta zauna.

Dan rainin hankali shi ne ka wani shareni kamar baka ganeni ba, to wurinka na zo magana nake so muyi, ta fada tana kokarin kakaro murmushi. A ina kuma kika san wannan sunan nawa.

Na tambayeta Wane suna kake magana? Ta tambayeni ita ma. Dan rainin hankali mana. Na fada mata Dariya tayi har sai da kyawawan hakoranta suka bayyana.

Au! Dama sunanka ne kenan? Kai dai ko yaushe baka rabo da abin dariya. Na gode amma zai fi kyau kiyimin bayanin ko ke wace ce? Na fada ina kokarin rufe babin
wasar da take kokarin budewa. Na san ka san ko ni wace ce, amma tunda ka nuna baka sani ba zan kara sanar da kai,
fateema ce. Kona ce fateemar ka ce Ta sanar dani. Wace fateema kenan? Na sake tambayarta.

Haba my one kar ka mun haka please, yanzu ashe duk soyayyar da kake nunamin a waya yaudara ce ba sona kake yi ba? Ta fada cikin murya mai rauni.


Look! Fateema ba fa zan yarda ki sake jefani a wani bala’i ba, ba ni kadai ne saurayi a garin nan ba, zai fi kyau ki je ki nemi wani ki kara yaudararsa ni wacce kika yimin ta isa haka. Ka tsaya ka fahimceni Kudancy ba wata yaudara tsakaninmu. Ta fada tana kokarin tabbatarmin da abinda ta fada har cikin zuciyarta ne.


Dago fuskata nayi na kalli fuskarta ga mamakina hawaye na gani suna sartu a kan kyawawan kumatunta. Hawayen sun karayar dani amma sai na dake.


Fateema kenan, abinda baki fahimta ba shine an dade ana ruwa kasa na shanyewa. Kalamanki na yaudara ba zasu kara tasiri a gareni ba. Yanzu ke ko kunya ba zaki ji ba da aure a kanki ki rika bibiyar samari kina jaza musu fitina? ka daure ka saurareni Kudancy Wallahi gaskiya zan fada maka. Tace dani Ina jinki.

Tasowa tayi daga inda take zaune tazo dab da telata, kusancin dake tsakaninmu har sai da na rika jin bugun numfashinta. Ka kalli kwayar idona ka fadamin idan ka ga yaudara a ciki.

Ta bukaceni. Idan kin manta akwai bukatar na tunatar dake cewa ke matar aure ce fa, saboda haka kawai ki fadamin abinda kike son fadamin ina saurarenki. Kayi hakuri da masifar da na jefaka, da kuma boye makan da nayi cewa ni matar aure ce, ban yi haka don in cutar da kai ba, nayi ne saboda na san idan har na sanar da kai ni matar aure ce ba zaka kulani ba. Kuma ban san mijina ya dakeka ba sai daga baya, da ba yanda za’a yi na bari hakan ta faru, na san babu yanda za’a ka yarda da zancena idan har ban sanar da kai ko ni wace ce ba.

Ina jinki…. Nace da ita saboda kalaman nata na yaudara sun fara isata. Kwamanda bai maka karya ba ni matarsa ce, amma ba na sonsa ba kuma da son raina na aureshi ba, iyayena ne suka auramin shi saboda la’akari da mukaminsa da kuma dukiyar da yake da ita, basu yi la’akari da cewar bana sonsa ba, kuma me zai je ya dawo bayan auren. Me yasa bakya sonsa? Na katseta da tambayata. Baka bukatar dogon bayani Kudancy, ba sai na fada ba kai kanka kasan kyakkyawa kamata bata dace da tsoho mai tarin shekaru irin na Kwamanda ba.


Na tsinci kaina a cikin kunci bayan tarewata a gidan Kwamanda, ba wai ya gaza wajen bani jin dadin duniya ba ne, ko daya, kawai dai na tsaneshi ne, wannan ne yasa ni fadawa a social network ko zan hadu da kawaye masu debemin kewa.
Lokacin da na fara facebook shafukan bayar da dariya da saka nishadi nayi ta nema ina shigarsu, a garin lalubena ne na ci karo da kai wata kawatace taban labarin indai labari nakeso na nemi MASARAUTAR MASOYA nasha labari, Kuncin da nake fama da shi ya ragu, saboda labaran da nake karantawa a wadannan shafukan, sai dai duk cikin shafukan ba kamar naka domin kai gwanine.

Kai DAN’ZAKI NE wane yaro Lokacin da na fara cin karo da lambarka ta WhatsApp ba karamin farin ciki nayi ba saboda naga hanya mafi sauki da zan rika samun labaranka. Yawan karanta labaranka da nake yi, sai naji ka fara birgeni, sannu a hankali sai naji na kamu da sonka. Ba karamar barazana na fuskanta ba Saboda na san ba abu ne mai yiwuwa ba nayi soyayya da kai alhalin da aure a kaina,

GUYS zamu ci gaba gobe a Kashi na 6 insha Allahu.

Ab Kudancy

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »