Tarihin Abba John Na Kwana Casain.

0 313

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abba sa’ad wanda aka fi sani da “Abba John” A shirin Kwana Casa’in, wanda wasu ke kiran sa da “Abba s Boy” musamman a harkar sa ta waka, wasu kuma sunfi sanin sa da “Bigi waladun”.

An haife shi a ranar “29 ga watan Aprilu” a garin SAMINAKA dake karmar hukumar Lere a Jihar kaduna dake Nigeria ya girma ya Kuma yi karatunsa duka a cikin garin na Saminaka wanda a yanzu ya kasance mazaunin cikin garin kaduna.

A tattaunawar da akayi dashi tare da manema labarai akan yadda ya tsinci kansa a harkar film ya bayyana cewa shi a rayuwarsa Allah yayi shi mai son Bayyana basirar sa da gwada abubuwa wadanda yake da basira akan su da farko waka yake yi wanda daga baya yazo yana yin comedy, a hakan yayi sha’awar shiga harkar wasan kwaikwayo na “Dadin Kowa” wanda Arewa24 ke haskawa a lokacin ya sami director na wannan film ya bayyana masa kudirinsa anan ya bashi hakuri sakamakon lokacin film din yayi nisa a inda yayi masa Albishirin Akwai film wanda nan gaba kadan idan lokaci yayi zai nemeshi domin yin Audition (Tantancewar shiga) film din.

Bayan wasu lokuta aka kirashi domin Audition (tantancewa ) kuma inda yayi nasara aka Bashi Role na Abba John a shirin da za’ayin mai suna Kwana chasa’in.

TAMBAYAR DA MUTANE DA DAMA KEYI AKANSA WANDA YAKE KARO DASU A SOCIAL MEDIA.

Mutane da dama suna yi masa kallon ba musulmi ba, sakamakon role din da yake takawa a shirin mai dogon zango na Kwana Chasa’in, inda wasu ke yimasa tambayan akan shi musulmi ne ?

Tabbas Abba Sa’ad wanda akafi sani da Abba John musulmine kuma cikakken Bahaushe

TASIRIN DA SHIRI MAI DOGON ZANGO NA KWANA CHASA’IN YAYI A RAYUWARSA

Hakika wannan shiri yayi tasiri sosai a cikin rayuwarsa inda ya bayyana cewa: wannan shiri yayi sanadiyyan samin dubbannin masoya a gareshi marasa adadi sanan yayi sanadiyyan haduwar sa da manyan mutane wanda sun wuce level dinsa amma sanadiyyar wannan film suna alaka har suna kiransa sannan ya daukaka darajarsa sannan akwai abubuwa da dama wanda bazai mantasu ba wadanda sanadiyyar wannan shiri na Kwana Chasa’in, akwai ranar da yaje zaiyi international passport a Immigration Office dake Kaduna wanda a wannan lokacin zuwansa kafin kace me saiga mutanen wajen suna ta murnar ganinsa da yin hotuna dashi wanda cikin sauki yayi abinda ya kawoshi hakan ba karamin nasara bane a gareshi,

RA’AYINSA GAME DA HARKAN FILM.

Ya bayyana cewa a yanzu baya yin aiki a karkashin masana’antar film ta Kannywood duk da zai iya yuwuwa yayi ko nan gaba indan wannan project din ya samu amma shi baya cusa kansa akan abinda bai zama dole ba a kansa idan Allah yasa kaddarar sa zaiyi, to tabbas hakan saiya faru.

GWANIN SA A HARKAN FILM NA KANNYWOD.

Kowa dake Kannywood gwani nane cewar Abba John inason kowa kuma kowa yana birgeni sosai, sanan ya bayyana Hadiza Gabon da Fatee S.U a matsayin Jaruman sa.

BABBAN BURIN SA A RAYUWA

Burinsa a rayuwa bai wuce yaga ya kawoma mutane cigaba ba ta kowanne fanni matukar Allah ya bashi daman hakan, inda yayi musali da harkan film, yace akwai mutane da yawa da suke saminsa domin nuna sha’awan su da shiga harkan film basusan ta yadda zasu fara ba, kuma shi baiyi karfin da zaice zaiyi film nashi kuma yasa mutum ba, yace zaiso ace shima gashi yakai level din da zaiyi nasa kuma kamar yadda aka bashi dama ya taka rawarsa a wannan shiri na kwana chasa’in shima ace yaba wasu dama a karkashinsa ace wasu sun daukaka ko cimma wata nasara a rayuwa sanadiyyan sa

ABINDA YAFI BATA MAI RAI

Ya bayyana abinda yafi batamai rai a rayuwa inda yake cewa “Yin kazafi ‘ a fadi abinda bai fada ba hakan ba karamin batamai rai yake ba matuka.

ABINDA YAFI SANYASHI FARIN CIKI

Sanannan ya bayyana abinda yake sanyashi farin ciki lokaci zuwa kokaci wanda yace shigowar creadit Alert (Shigowan sakon wasika na kudi daga asusun sa na banki) hakan ba karamin faranta masa yake yi ba.

Daga Bakin Mai Ita BBCHAUSA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »