Bani Da Lafiya Kashi Na Sabain Da Bakwai (77)

0 535

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

“Lallaikam ya zama wajibi ga duk wani magidanci ya tabbata ya iya kuma ya haddace Addu’ar da ake yi yayin kusantar iyali saboda samun kariyar ALLAH wa jaririnsu daga sharrin Shedan.”*

Malamar ta amsa da cewa:  Ai zahirin Hadisin da yazo shi ne namiji ne zai karanta Addu’ar ba mace ba, amma wasu malamai sun tafi akan cewa idan macen ma ta karanta bayan mijinta ya karanta wanna ba matsala saboda kowanne cikin mata da mijinta za su iya nemarawa yaransu tsarin Allah daga sharrin shedanu.

Malama ta kara da cewa: Amma dai a nunawa maigida muhimmancinta a sanya shi ya haddace ta kuma ya rika karanta ta a lokacin da akace a karantata din, hakan zai fi dacewa kuma zaifi zama sawaba Allahu A’alam.

Mai gabatarwa: Na’am Malama muna godiya sosai kuma ALLAH yasaka da Alkhairi. AMEEN.

Malama: Sannan daga cikin ababen da yakamata mu lura da su kuma mu kiyaye su a lokacin da mace ke dauke da Juna biyu tun a watannin farko su ne kamar haka:

  • Yawaita Addu’ar Allah ya kare kuma ya kiyaye  jaririn da kike dauke da shi a cikin ki daga sharrin halittunsa.
  • Yawaita sauraro da karanta Alqur’ani iya yadda a koda yaushe. Da kuma karanta wasu Ayoyin Alqur’ani ana sha.
  • Kauracewa sauraron kade-kade da wake-wake.
  • Daina fitar dare, sai idan da wata lalura mai karfi.
  • Mai ciki ta daina yawan wucewa ta cikin maqabarta ko a gefenta, saboda Jinnu za su iya shafar cikin.
  • Ana son mai ciki ta rika boye cikinta, ta daina yayatawa kowa a social media cewa tana dauke da juna biyu sai idan har ya bayyana ga mutane, ( saboda akwia mahassada da amsu Kambun-baka kuma za su iya yiwa juna biyun illa.)…

Sai wata mata tayi tambaya tana cewa: Shin Malama iya wadannan ma sun wadatar ko kuwa akwai wasu abubuwa ne da zamu rika daurawa ko naqalawa a jikin mu domin samun kariya daga sharrin Mayu da masu Kambun-baka?

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji shin akwai abubuwan da suka halasta ne ga mai ciki ta rika daurawa ko maqalawa sbd samun kariya daga sharrin Mayu da Kambun-baka?)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »