Aisha Talba Kashi Na Daya (1) (Hausa Novel)

2 205

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

20221119_095717.jpg

Kashi Na Daya 1

Sunana Abdulrazaq Ahmad ( KUDANCY ), kuma a yanzu Shekaruna ashirin zuwa sama abisa al’ada dole ne a rayuwa mutun sayya fuskanta wata ‘yar chakwakiya, kamar dai yadda arayuwata na fuskanci wata babbar chakwakiya wadda hakan ta canja man rayuwa.


To atakaice dai musoma daga farkon zancen,

Shekaranmu daya da wata biyar muna chatting da wata yarinya mai suna Aisha Mu’azu Aliyu Babangida, nida ita munshaku da juna sosai tana mahaukacin sona before muhadu kwatsam sai wata rana ta kira ni a waya dana dauka na ce,” “Hello Gimbiya ta ina fatan kina cikin koshin lafiya?


Tayi murmushi ta ce,” “Lafiya klau baby na, ina fatan kaima zanji haka daga gare ka?
Nayi murmushi na ce,” “Ai daga jin muryata ya kamata ki fahimci hakan,”Naji dadi kasan me nake so dakai yanzu?


Na gyara zama na ce,” “a’a sai kin fada,” Ta ce,” “Kaga shekara daya kenan da watanni muna tare amma banda muryar juna bamu ta6a ganin fuskokin mu ba,” Na ce,” “To meya kawo wannan zancen rashin ganin juna? Tayi murmushi ta ce,” “Kada kadamu bawani abu bane kawai ina so ne muhadu da juna yau,” Na fiddo ido na ce,” Haduwa kuma, to a ina?


Ta ce,” “A Kpakungu cikin KOWA SCHOOL gobe misalin karfe 12:00pm amma kafin nan ya kamata kasan yarinyar da zaka hadu da ita,” Na gyara zama domin kuwa zanji bakon abu aguna tunda muke da ita banta6a sanin ita ‘yar waye ba kuma ban ta6a tambayar ta ba domin ni don Allah nake sonta badan komi ba kuma bata ta6a nuna man ita yarinyar me kudi ba ce, amma kuma ni ban 6oye mata komi ba tasan cewa ni ba dan masu kudin da za’azo agani ba ne amma tasan muna da wadata sai na ce,” “To ina jinki gimbiya,” Sai ta ce,” “Kasan ni ‘yar waye?

Na ce,” “A’a sai kin fada,” ta ce,” “To ni ‘ya ce ga Dr Mu’azu Aliyu Babangida Talban minna wato tsohon gomnan daya sauka,” Sai nayi murmushi domin kuwa haduwa da irinsu aguna ba abu bane bako,” Sai tayi shuru ta ce,” “Meyasa bakayi mamaki ba? Sai na ce,” “Nayi mamaki mana amma daga ta ciki ne zan jira ki a kowa school din Allah ya kaimu anjiman,” Tayi murmushi ta ce,” “Ameeeeen,” mukayi sallama da ita nakashe wayana sannan nafara nazarin yadda zan 6ullowa haduwarmu amma dole naje mata ashigar girma,”


Na ciro wayata na kira Abokina Sameer ba mujima dayin waya ba sai gashi ya shigo dakina yazauna kusa dani ya ce,” “Mutumina ya akai?


Na ce masa,” “Lafiya lau yau zan hadu Aisha Dr Alh mu’azu Aliyu Babangida Talban minna misalin 12pm,” Sameer ya fiddo ido ya ce,” “Kananufin yarinyar Talba? Na ce,” “Eh amma ina so nayi mata shigar girma kuma kasan gobe su daddy zasuyi tafiya shida mummy zuwa yola bikin Kanin mummy kuma sati daya zasuyi kuma kaga dole a mota zasuje,” Yayi murmushi ya ce,” “To basai kahau daya daga cikin motocin ba,”

Na dan hararesa na ce,” “Kai bana so naje mata da motocin gidanmu ni dai na aro nake bukata zan biya konawa ne indai zan fita kunya,” yakalleni ya ce,” “ba Matsala za’asamu aron amma kowace mota ka bada 7,000 kaga guda biyar zai kama 35,000 ya kace?


na mike cikin sauri na dauko masa 40k na mika masa tare da cewa,” “Kai hada na oil don haka ku biya gidan mai amma tare zakuje kai da abokanka kuma kafada masu yadda za’ai kada suyi man raini agaban yarinyar nan kuma su kwantar da kansu suyi biyayya, ya tafi tare da cewa,” “To (KUDANCY),” Tunda naga ya fita ni kuma nashiga bandaki nawatsa ruwa sannan nafito, Farar shadda ce riga da malun malun nasa ajikina na dauki kuma farar hula nasa shaddar taji aikin wuta na fesa turarukana masu kanshin tsiya,”

Misalin karfe 11:35am Sameer da Abokanansa suka shigo da motoci farare kuma duk kamfaninsu daya Mercedes ce masu kyau sukayi parking a harabar gidanmu,”
Ya daga waya kira ni wanda dama zaune nake ina jiransu, ina dauka ya sanar dani suna waje, cikin sauri natashi nafito sai naci karo da salmah ta kalleni ta ce,” “La yaya ina zuwa?


Na harareta na ce,” “Wani gu zani,” har zan wuce ta ce,” “To shi wurin baya da suna ne da baza afada man ba? najuya ko waigowa banyi ba na ce,” “To dola ne nafada miki wurin dazani kinga tafiyata nasakai nafita nahadu dasu Sameer shida abokanansa su hudu da Habeeb da kamal da Ameer da faruq sai na biyar din wato sameer,”


Sameer yabude man mota nashiga gidan baya muka wuce, abun gunan sha’awa idan kammu,” Bamuyi minti goma ba sai gamu a kofar kowa school hon mukayiwa me gadi ya bude gate din muka shiga filine makarantar take dashi sosai mukayi parking ba tare munfito ba kowannenmu yana cikin mota yana dakon zuwanta musanman ma ni nida namatsu da na ganta,”Muhadu a Kashi na biyu,
Zamuci gaba a part 2 gobe in Allah ya kaimu

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Protymah says

    Uhmm. Very nice story ☺️

    1. alummarhausa says

      @

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »