Takaitaccen Tarihin Ali Baba Yakasai

0 170

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ali-baba-Yakasai.jpg

Ali Baba Yakasai, na daya daga cikin music producers na arewacin Nigeria, An haifeshi ne a unguwar Yakasai inda yayi Primary School a Yakasai yayi karatunsa na Secondary a G.S.S KWALE Sannan yayi karatun na gaba da Secondary inda yayi Diploma a fannin Management Studies Sannan yayi HND a Management Studies inda ya karanci Public Administration.

Ali Baba ya fara harkar kade-kade da wake-wake tun shekarar alib 1987 wanda har zuwa wannan lokaci na 2022 a cikin wannan harka yake.

Harkan kade-kade da wakoki abune wanda yake abin sha’awarsa tun a yarinta, yafara harkar kida akan mandirin yabon Manzon Allah (S.A.W) inda yake yima Alh. Bashir Dan Musa Kida na Mandiri na wakokinsa daban-daban, hakan shine ya sanya ya kara samun gogewa akan sanin yadda zai sarrafa instrumental na kida da sanin inda zai ajiye kida a cikin gurbinta.

Sannan ya bayyana kidan daya buga na wakar Sangaya a matsayin kidan da ya fara fice a kide-kiden sa wanda bama shi kansa ba hatta film din wakar hausan wannan waka ta kara tallatashi.

A wata tattaunawa da aka yi dashi a BBC HAUSA ya bayyana abinda yake sanyashi farin ciki sosai wanda bazai taba mantawa ba.

Yace: Akwai wata rana wanda nake ta tunanin yadda zanyi na hada kida domin a wannan lokaci kwana na keyi da abin kida, shi wanda ya kasance maigida na wanda shine ya koyar dani kida banyi kwariba Allah yayi masa rasuwa shine Nasiru Ishaq Gwale A haka nake ta kokari ina tunanin yadda yake yin wani abu sannan ina kunna kidan sa a haka ina gwadawa, to babban abinda yayimin dadi shine ranar da nazo na buga kida kuma naga ya hau sabanin baya wanda nakan dade ban hada kida ba to a wannan ranar nayi farin ciki kam sosai matuka.

Sannan ya bayyana Jindadin sa sosai da godiya ga Allah akan basirar daya bashi wanda har yakai ga ya iya wani abu wanda zaiyi mutane su yaba kuma harma su iya sanya kudi su sayi wannan abu hakan ba karamin nasara bane a gare shi, kuma yadda mutane suke yabawa kuma akeson aikin nasa hakan ba karamin sanyashi jindadi yake ba sakamakon wasu zasu yi amma ko sauraron su ba’ayi.

Sannan ya bayyana abinda yake bashi ta’ajibi wanda yace Butulchi, wanda mutane zasu zo maka da niyyan koyan sana’arka ka rike su hannu bibbiyu ka koya musu sana’ar ka ba tare da nuna mugunta ko wani abuba bayan mutum Allah ya bashi Albarkar dake cikin abin ya dawo yana yima gadara da kaskantar dakai don kawai Allah ya bashi abinda kai bai baka ba.

To wannan halin idan ya tunashi yana bashi mamaki sannan yana bashi haushi wani lokaci.

Shirin Daga Bakin Mai Ita BBCHAUSA.

Musa Badamasi Musa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »