Rayuwar Fateema (Kashi na 3 Hausa Novel)

0 108

RAYUWAR FATEEMA PART 3 (True Life Story)Umma tayi sauri ta kwace wayar daga hannun Phateema domin bataso Yaya Mujaheed yasan halin da Muke ciki, tayi magana cikin karfin hali tace lpy lau Mujaheed, Mujaheed yacewa Umma Wai meke damun kanwata,? Umma tace tana kukane saboda rashin ganin ka akusa damu,

Yaya Muhajeed yace to inbanda abin sister ai saura wata bakwai nadawo, yace umma bata wayar na lallashe ta umma ta mika wa Phateema wayar tare da yi mata nuni akan tadaina kukan data ke Phateema ta karbi wayar, yace sister kiyi hakuri kinji zan dawo nan bada dadewa ba, Phateema tace yaya wallahi kullum haka kake cewa, Mujaheed yace to sister wannan karon dai tinda nace nakusa dawo wa to nakusa kinji?

Tace to yaya, Mujaheed yace yanxu kina Ss3 ko? Tace eh yaya, to ki maida hankali kinsan nurse nakeso kixama, tace to yaya, yace Abdulrazaq sun gama waec dinsu last week ko? Tace eh, yace to kice masa yadage sosai, tace to, yace yauwa sister bye, tace bye yaya, ya katse wayar,

Can kuwa a bangarena tuni nayenke shawarar tafiya gidan kakannina na bangaren uwa bayan na isa gidan na kwashe duk abinda ya faru na fada musu nan mahaifin umma yace kayi zamanka ko gidan kada ka kara zuwa ni zan dauki nauyin karatun ka shikuma abban naka xan neme shi, Ni kuma naci gaba da karatuna ba abinda yake damuna sai dai idan natuna halin da umma da Phateema suke ciki,

A duk sanda mukai waya da yaya Mujaheed sai naji kamar nafada masa halin da Muke ciki amma idan na tuna gargadin da umma tayi mani akan kada na kuskura na fadawa yayan namu, sai kawai nafasa fada masa,

Amarya da kannenta Aliyu da Hafsat suna xaune a falo, Aliyu yace aunty nifa gaskiya yarinyar nan nake so, amarya tace wace yarinya? Abdul yace “yar kishiyar ki mana Phateema, amarya tace ai dama tunda naga take takenka nasan akwai magana, don haka kada kaji komai kamar ka mallaki Phateema ka gama, Aliyu yayi tsallen murna yace thank you aunty, Hafsat tace ikon allah ni banga abinso ajikin wannan yarinyar ba, amarya tace ina ruwanki?

Hafsat tace ba ruwana, dare yayi abba yadawo ya shigo gida tare dayin sallama umma ta amsa tace ta tashi domin karbar kayan da suke hannusa, ya daka mata tsawa tare dacewa ina ruwanki da kayana? Umma taja da baya, abba yamika wa amarya kayan amarya ta karba’ tare da yiwa umma gwalo, abba yajuyo yacewa umma duk da cewa yau kwanankine inaso kiyi hakuri domin yau adakin amarya nake son kwana, yajuya ya nufi dakin amarya batare da yatsaya jin amsar da umma zata bashi ba sun zauna shida amarya tace alhaji akwai maganar dana keso nafada maka, abba yace ina sauraronki, amarya……..

MUHADU A PART 4 GOBE IDAN ALLAH YAKAIMU

Ab Kudancy

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »