Rayuwar Fateema (Kashi na 4 Hausa Novel)

0 170

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RAYUWAR FATEEMA (TRUE LIFE STORY)

PART 4 (Babi Na Hudu)

AMARYA ta gyara xama cikin kisisina tace dama wallahi yaron nanne Aliyu yace yana kaunar Phateema shine nikuma nace masa ya kwantar da hankalinsa kamar yasamune, abba yace ikon allah to ai Phateema “yarki ce kuma duk hukuncin da kika yanke akanta dai-dai ne, amarya tace yauwa alhaji shiyasa kullum nake kara son kasancewa da kai, abba yace nima haka, amarya tace amma yakamata kasanarwa da yarinyar da mahaifiyarta don kada inyi magana abin yazama rigima, abba yace nida “yata akwai wanda ya isa yayi min iko da ita don haka kice masa yasameta yayi mata magana, amarya tace nagode alhaji.

Da safe abba yakwalah wa Phateema kira, ta amsa taho da sauri domin kuwa yanzu duk duniya ba wanda take tsoro sama da abba da kuma amarya, taxo ta tsugunna tace abba gani, yace saura wata nawa kigama secondary? Wata takwas abba, abba yacewa Phateema to nayi miki mijin aure, agigice Phateema tace abba aure?? Abba yace eh kuma bawani bane sai wannan yaron Aliyu, abba bai tsaya jin amsar Phateema ba ya tashi yayi waje, umma wacce take jin duk abinda yake faruwa taxo ta kama Phateema suka shiga daki umma tai ta lallashinta,

Phateema tace umma idan akwai wanda natsana aduniya bewuce amarya da danginta ba, gsky umma yakamata yaya Mujaheed yasan halin da muke ciki, umma tace in banda abinki shima yayan naku ai akarshin abban naku yake, kuma in kin kwantar da hankalinki saura wata biyar yadawo kiyi hakuri, Phateema ta sake fashewa da kuka mai tsanani,

Yau gari ya waye umma ta tashi tana cikin matsanancin zazzabi don haka tashirya domin zuwa asibiti, bayan abba ya shirya, suka taho shida amarya zata rakashi mota, tana tafiya tana ta wata yangar banza, umma ta karasa, tace yauwa alhaji dama so nake ka ajeni a asibiti, abba ya juyo yaharareta, yashiga motarsa batare daya kula da umma ba, yaja motarsa yana yiwa amarya bye bye itama tana yimasa, amarya ta juyo tayiwa umma dariya, umma tafito tanemi adai-daita sahu ta tafi asibiti,

Phateema ta fito daga wanka matsanancin ciwon da kanta yake mata shiya tilasta mata xama akan gadon ta tayi tagumi hawaye ne yake gangarowa daga idanunta, jitai ana turo kofar dakin nata, ta tashi da sauri domin ta samu abinda rufe jikinta, amma kafin takai ga yin hakan tuni yashigo, Aliyu tagani yashigo yana mata murmushi, cikin fushi tace kai mahaukacin inane zaka shigowa mutane daki? Murmushi yaci gaba dayi tare da kura mata idanu, saikace mai kallon TV, kunya tagama rufe Phateema saboda daga ita sai daurin kirji, a hankali taga Aliyu ya fara matsowa kusa da ita, tafara ja da baya, tana bashi hakuri akan kada ya cutar ita, shikuwa dariyar mugunta kawai yake yana kara kusantar ta,

Phateema tana ja da baya, shikuwa Aliyu yana kara kusantar ta hardai taje karshen bangon daki, Aliyu yayo kanta gadan-gadan, Phateema tana dubawa gefanta taga wukar da umma take amfani da ita, batayi wata-wata ba ta dasa hannu ta dauko wukar nan ta nuna Aliyu da ita, tace kada kamatso wallahi zan caka maka wukar nan, wanda tuni idonsa ya rufe yayo kan Phateema, ita kuwa batasan sanda ta labta masa wukar nan akai ba, Aliyu ya kwalla kara a zube akasa, amarya da Hafsat suka jiyo karar Aliyu su taho aguje, ita kuwa Phateema tuni ta rude sakamakon ganin yadda jini ke zuba daga kan Aliyu, su amarya suka karaso suna zuwa sukaga Phateema rike da wuka a hannu, basuyi jinkirin kiran abba ba tare da daukar Aliyu zuwa asibiti,

Bayan sun karasa asibiti ne, likita ya fara duba Aliyu, su amarya da Hafsat suna zaune sunyi tagumi, alhaji ya shigo arude, ya nufi wajen likita, yace likita yajikin nasa likita yace da sauki, domin yanxu anyi masa duk abinda ya dace saboda haka zaku iya komawa dashi, alhaji yabiya kudin komai, sannan yadauko su a motarsa yana tafiya yana xage-xage akan Phateema, Amarya tana kara xuga shi, Ita kuwa Phateema tuni hankalinta yagama tashi domin sanin abinda zai biyo baya, tayo waje domin barin gidan kafin abba yadawo, tana zuwa kofa sukai karo da umma, umma tace lapiya Phateema?

Phateema ta fada mata duk abinda ya faru’ don haka umma tayi saurin bawa Phateema kudin mota, umma tace kiyi sauri kitafi gidansu kaka idan abin ya lafa saiki dawo, Phateema tace to umma, aiko min da kayana na.makaranta, umma tace to, Phateema tayi waje, kana ganinta kasan arude take, Umma tana zaune tayi tagumi, taji shigowar su alhaji ko sallama babu sai masifa yake, yashigo dakin umma yatsaya akanta, yafara magana cikin fushi, Ke ina wannan “yar iskar yar taki?.

Maganar tayiwa umma xafi matuka, hakan yasa mikewa cikin fushi, tace alhaji duk abinda zakai kada ka kara kiran “yata “yar iska, ga “yan iska nan kana tare dasu wannan yaron yayi kokarin yiwa “yarka fyade amma kuma sai gashi kai kake kare……… Saukar mari umma taji a fuskar ta, tana dubawa taga amarya ce ta zabga mata mari, itama batayi wata-wata ba ta daga hannu ta sharara mata mari, abba dake tsaye yana kallo tuni shima ya daga hannu zabgawa umma mari wanda sai da ya tilastawa umma dafe kumatu, umma ta fashe da kuka mai tsanani wanda duk wanda yaji dole ya tausaya mata, alhaji ya kara da cewa kuma idona idan Phateema sai na karya ta, suka juya suka fice daga dakin suka bar umma tana kukan bakin ciki, Phateema bata tsaya ko ina ba sai gidan kakanninta ta fada musu duk abinda yafaru, hakan yasa kakanta yace gaskiya abin nashi cigaba yake don haka bari naje wajen malam nasanar dashi abinda yafaru,

Bayan dare yayi amarya da abba suna zaune, abba yana ta lallashin amarya amma taki, sai abba yace kifadi abinda kike so nayi miki komai wahalarsa don ki daina fushin nan, amarya tayi murmushi da alama taji dadin maganar abba, sannan tace ni abu hudu nakeso, alhaji yace fade su duka indai kudi ke yinsu kamar angama ne, amarya tace 1 inaso kadawo min da yan uwana mutum takwas gidan nan da zama 2 inaso ka cika min alkawarina na motar da kace zaka sai min 3 inaso mufita yawon bude Ido shakatawa, na hudun kuma baxan fada ba sai mun dawo daga shakatawa, abba yace wannan duk mai sauki ne indai zaki huce, don haka gobe zan tura driver ya dauko “yan uwan naki, mota kuma muna dawowa xaki ganta, don haka wani state Kike so mu tafi?

Amarya tace Abuja, abba yace to kada kidamu tawan, farin ciki ya lullube ta, Abba ya gama shirin tafiya Abuja shida amaryarsa gida kuma ya cika da “yan uwan amarya, wanda yanxu su goma ne tara daga ciki dukkansu maza ne majiya karfi daya ce mace wato Hafsat, sai sharholiyar su suke kamar gidan ubansu, umma kuma bata da damar sakewa haka umma tayi ta hakuri tana lissafin dawowar ɗanta Mujaheed wanda kullum takeyiwa addu’a, Yaune ranar tafiyarsu abba da amarya Abuja don haka ya tara kowa nagidan, yafara jawabi kamar haka:- kamar yadda kuka sani yau zamu tafi, to don haka duk abinda kuke so ku tambayi wannan matar ya nuna umma, wadda kanta yake a tsugunne, yace kuma idan kika sake naji ance kin fita to allah ya isa, Hafsat tace alhaji yaushe kuma zaku dawo? abba yace bazamu wuce 3 weeks ba, bayan dawowarsu ne umma tafara fuskantar wulakanci kala-kala, badon allah ya isar da alhaji yayi akan fitar ta ba da ba abinda zai zaunar da ita A gidan,

A kwana a tashi yau saura 2 weeks Mujaheed ya dawo Zaria domin yayi gagarumar nasara anan akayi posting dinsa ya kagu domin ji yake kamar ya janyo ranar domin yansan ganin su umma da Phateema da Ni, Rashin mutuncin da “yan uwan amarya suke wa umma ya tsananta, umma tana ta hakuri da jurewa, yau saura sati daya su abba su dawo daga Abuja, Bayan dawowarsu abba da kwana daya abba ya siyowa amarya dalleliyar mota mai suna ( Toyota venza), ya bawa a marya mukulli, tayi murna sosai da motar taki hawanta tace sai ranar dab zata unguwar kece raini, haka aka bar mota sabuwa kar a ajiye, umma tace to alhaji kacika min alkawari saura daya danace sai mun dawo, abba yace wanene?

Amarya tace ya kira umma tukunna, abba ya kwalawa umma kira ta taho da sauri, tana zuwa ta tsugunna agaban abba, Amarya tace alhaji sonake kasaki wannan matsiyaciyar ta nuna umma, umma ta dago kai a da sauri, shima abba agigice yace saki!!!? Amarya ta fashe da kukan munafinci tace yanzu alhaji zaka iya karya alkawarina, abba yace yi hakuri, yanda kike so haka za ayi, yace wa umma na sake ki saki 1 batare da ya iya hada ido da ita ba, umma tafashe da kuka mai tsanani, wanda duk wanda yaji sai ya tausaya mata,

Amarya tasa kannen ta sukayita watsi da kayan umma, umma ta koma gidansu suka hadu gata ga Phateema ga Ni, Yau ne allah yayiwa Yaya Mujaheed dawowa. NDA ya taho da “yan rakiya ta mota uku na sojoji, Ya dauko hanyar Zaria, baisanar da umma yau zai dawo ba sakamakon yafison muyi mamakin ganinsa suna tafiya har suka shigo Zaria..

Muhadu a Part 5 KARSHEN LABARIN Gobe idan Allah yakaimu.

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »