Hirar Masoya

0 160

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

HIRAR MASOYA❤


Sír Ab Kudancy II : Amincin Allah madaukaki me yin yadda yaso ya tabbata agareki yake wannan gimbiya me Amsa suna MAI MATSAYI NA DAYA ARUHINA

Khaleesaart : Amin my Abarbality da fatar kasamu daddan barci kuma katashi lafiya.

Sír Ab Kudancy II : Hmmm ai my love tinanin tauraruwar fuskarki bazai bari nai barci ba domin son da nake maki na daban ne.

Khaleesaart : Hmmm Shin masoyina izuwa yanzu ko ka fara jin gajiya a jikinka kuwa? Saboda ka kasance kana motsi acikin zuciyata a tsawon dare ka kuma kasance mai zagaya dukkan jikina ta kafar da jinin jikina ne kawai yake gudana a cikin kowace safiya da yini.

Sír Ab Kudancy II : Hakika sabo wawan abune,baiyi shawara daniba lokaci guda naji nasaba dake tamkar wacce nadau tsawon shekaru muna tare,to meye sirrin?shin hasken kwayar idanunki ne,ko kyautatawarki gareni?
Kallo daya tak naimaki nan take sai naji tamkar indawwama ga kallon KYAKKYAWAr fuskar dana gani,wacce ta taro dukkan wasu shika-shikai na kyau,nayi mamakin ganin yadda nake shirin afkawa dajin dake cike da SARKAKIYA,dajinda kowa ke tsoronsa,saidai hankalina ya kwanta ne tun daga lokacin da nagano cewa kinada nutsuwa da girmama mutane,nasan zaki kawo guzuri gamai shirin tunkarar bakin daji mai nisan tafiyar da ba’asan iyakarsa ba,mai cikeda bishiyar farin ciki.

Khaleesaart : My real one ko da yaushe qwayar sonka na qara hayayyafa acikin xuciyata Duk saiwoyin xuciyata na qara girgixa tare da tashin amo mai yanayi na salon sunanka ne aduk lokacin da majiyata ta jiyo sunanka…..kaine buri kuma kaine gadon da na barwa xuciya domin ban ajiye komai ciki ba face xallar qaunarka.

Sír Ab Kudancy II : My sweety > An dasamin soyayyarki azuciyata kuma ta yad’u bisa jijiyoyin jikina dan haka ke kadai ce abokiyar rayuwa awajena,taltalin soyayyarki nakeyi domin kece wacce Ubangiji ya zab’amin amatsayin abokiyar rayuwata kisani cewa bugun zuciyata yana tafe da tasirin kasancewarki amatsayin wacce nakeso.

Khaleesaart : oh God ! !! Ya xanyi da rayuwata idan na juya dama da haguna ban jika kusa dani ba. Ina xansa rayuwata idan na wayi gari na rasaka,
Kai ne ka xamo jigo kuma garkuwar rayuwata ina sonka ina qaunarka.

Sír Ab Kudancy II : Me yasa idanuwana ke son zubar da hawaye duk sanda nazo kwanciya inhar bangankibi?Tun daga ranar dana fara ganinki a duniya duk wanda na kalla kamanninki shine cikin idanuwana koda na rufe ke nake gani. me yasa duk sanda naji sautin murya inhar ba taki bane bana iya jurewa?Ina zaki dani mai sona domin kace akalar dake cikin raina duk inda kika jani nan zan kasance.ke nake so Da wanne irin tasiri zan kwantanta a zuciyata?Kece kewar zuciyata kimin sassauci wajan hukunta zuciyata kan abinda da take nema gareki ma’ana soyyayarki.Ina kaunarki Kece alk’ibilana kece ke kawar da tunanina sanadin kyawun da Allah ya baki komi kyawun abu inhar kina tare dani bana iya ganeshi. Kece farin cikina ki duba halin da zan shiga sanadin kaunar da nake gareki wacce bani mafita kin shiga raina bazan iya kubuta daga soyayyarkiba muddin ina numfashi. Kece zab’ina kiyi kokarin sanya rayuwata cikin yanayin kauna cikin jin dadi mai inganci domin soyayyarki gareni bazan taba dainawaba.

Khaleesaart : Masoyina ko ka san cewa cikin kowace rana
kyawunka dad’uwa yake yi a cikin idanuwana?
Tabbas ba zan dakata daga begen kallon
kyakkyawar surarka a zahiri da kuma cikin
zuciyata ba har sai gobe hasken idaniyata, hmm!
karda ka manta a goben ma sai gobe. Ina son ka❤.kahutah lafiya.

Sír Ab Kudancy II : Ok my sweety ki kularmun da kanki.

Menene yafi burgeka acikin wannan hirar❓

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »