Rayuwar Fateema (Kashi na 5 Hausa Novel)

2 102

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

RAYUWAR FATEEMA

PART 5

Suna tafiya a kan titi duk inda suka zo sai kaga motoci sun basu hanya, yana cikin dalleliyar motar da yasa aka yimai order kafin Yataho, motocin sojoji biyu abayansa daya agabansa, kai idan kagansa bazakai tunanin soja bane, zakai tsammanin wani mai mulki ne, Suka karaso unguwar suna shigowa yaga layin ya canza mashi gaba daya, jama’a kallonsu suke suna tunanin ina zasu tsaya suka karaso kofar gidanmu, sojojine sukai saurin fitowa su wajen, Ashirin da biyar suka ka budemai mota yana fitowa suka kame, Suit ce fara ajikin Yayana Mujaheed, yasa black shoe dinsa ya sa space mai farar kwalba, ga agogonsa, diamond, kana ganin dressing dayayi kasan kafin yazama soja nigger ne, ya kalli jama’a da suka cika wajen kallonsa kawai suke, yaga abokansa dayawa aciki, take yakarasa cikin su suka gaggaisa sunata mamaki shikuwa tambayarsu yake, ya kowa da kowa? Suka amsa mai lafiya, yace bari nashiga naga su Phateema yanzu zanfito yaga duk sunyi sororo.

Yajuya ya sallami sojojinnan, suka nufi barrack dinsu dake Zaria, shikuwa yagoya jakar sa, ya nufi kofar gidan mu, gadan gadan, Yana shiga yaji hayaniyar mutane yarabka sallama, mazane sun cika gidan, suka juyo suka kalleshi, bawanda ya amsa, suka ci gaba da abinda suke, ya wuce dakin umma yaga anrufe, sai ya tambayesu dan allah ina umma?

kallonsa suke kawai ba wanda yacemai. Komai, waje yayo yashiga gidan su RUKKY domin sune makotan kuma itace yarinyar dasuke mutunci a unguwarmu, tana ganinsa tazo da gudu dan murna, tafara cewa oyoyo oyoyo ga Mujaheed ga Mujaheed yayi murmushin karfin hali Yace wai bazaki girma ba, tace au hakama zakace? Mamansu suka fito suka tareshi da murna, yatambayesu ko umma ta sanar dasu inda xata?

RUKKY takalli mama yaga sunyi shiru, RUKKY ce ta kwashe labari kaf ta fadamai, tuni yaji zuciyarsa tana tafarfasa’ yayo waje RUKKY tabiyoshi, suka shiga mota sai gidan kaka inda muke tare da umma, Suka karaso suna shiga sukai ido biyu da Phateema, a rude tace yaya Mujaheed su umma da su kaka suka juyo umma Phateema da Ni ne muka taso aguje shima shararawa yayi da gudu Yakarasa inda muke’ muka rungume juna kuka kawai muke, yace yanzu umma abinda yafaru akanku kenan amma ban saniba?

Umma tace dana banaso natada maka hankaline, nan dai muka zauna aka kawo mashi abinci yaci amma abincin daci yake mai, saboda zuciyarsa tana ta saka mai yadda zan ramawa umma ta abinda akai mana, Bayan kakanmu yadawone yace min abinda nakeso da kai kada kayi wani abu domin yanxu kana yimata wani abu mahaifinka zai iya tsine maka, saboda haka dole a fara warware kullin data yi masa, RUKKY ce tace nasan wajen wani malami mutumin kirki ne, ya juyo yace kada fa ki kaimu wajen boka, tayi dariya tace idan munje zaka gani, Suka karasa wajen malamin shida RUKKY,

makarantace babba, sukarasa akayi masu magana da malam, suka gaisa yayi masa bayanin komai malam yace to abinda nakeso daku ga wasu ayoyi zan baku ku karanta su aruwa kubawa mahaifiyar taku, da sunyi ido hudu duk wani sihiri xai lalace, domin dama ansa masa kiyayyar tane aransa, sukai godiya suka ba malam abin sadaka suka kamo hanya, suna iso wa RUKKY tayi abinda malam yace ayi ta bawa umma tasha, yamma tayi yadauko RUKKY yakawo ta gidansu, Washe gari da safe suka nufi office din abba Shida umma suna zuwa suka shiga kai tsaye, abba yana rubuce rubucensa, sunayin sallama ya dago kansa yana hada ido da umma kawai sai gani mukai ya fadi kasa, da hanzari suka karasa yakama abba wanda tuni yasuma, suka dauki abba sai wajen malamin nan, suna zuwa malam yafara karatuakan abba, cikin kankanin lokaci abba ya mike kamar ba shiba, suka hada ido da umma yace hajiya tace alhaji yace me ke faruwa?

Umma ta fashe da kuka, abba tuni hankalinsa yatashi, domin baisan abinda yasa Umma kuka ba, malam ne yayi masa bayani, akan komai, abba yayi kuka akamar karamin yaro, yarungume yaya Mujaheed yana kuka tare da bamu hakuri, tuni malam yayi bayani akan saki 1 da abba yayiwa umma’ aka daidaitasu, sukai addu’a suka tashi, abba yanufi office domin bai dakko motarsa ba, mukuma mukai gida, Tun muna mota umma taji yaya Mujaheed waya yana cewa akawo min sojoji kurata mota uku, umma tace lpy?

Yaya Mujaheed yace umma inaso muna Komawa gida ku koma gidan abba kedasu Phateema, umma tace to amma me zakai da sojoji? Yace umma inaso nayi musu hukuncine amma dan allah kada ki hanani, umma tace Mujaheed in banda abinka ai hakuri shiyafi, yace umma nasani amma zuciyata bazata gafartaminba idan aka ci mutuncinki nakyale, ahaka dai umma ta yarda da abinda yace’ muna karasawa gida su umma suka dauki kaya sai gidan abba, RUKKY ce tajagoranci shigarsu umma gidan, suna shiga yan uwan amarya sukayo musu ca!!! Amarya ce taxo wajen umma tafara cewa mara zuciya ansaketa amma ta dawo.

Phateema tayi caraf tace ke dallah can allah ya tona asirinki matsafiya kawai, Hafsat tace wa Phateema uwarki ce matsafiya, tuni Na daga hannu na zabgawa Hafsat mari nanfa fada ya kaure RUKKY kokarin kare umma kawai take, Yaya Mujaheed yana fitowa daga wanka yaji ana sallama dashi Yagama shiryawa kakin sojojine ajikinsa kamu nasa black spaces a fuskarsa, yana fitowa yaga kurata kowa da DG bellet a hannu sai muzurai suke, yayi wani murmushin mugunta yana xuwa kowa ya kame, suka hau motoci sai gidan abba, mutanen unguwa kuwa tuni kowa yafara dauko abin hawansa don ganewa idonsa HUKUNCIN yaya Mujaheed,

Rayuwar fateema

Suna zuwa ya sauko yakunna kai cikin gidan kurata suka takemai baya, jama’a kuwa sun taru sai kace taron daurin aure, yana shiga yaga wani yadaga hannu yana kokarin marin RUKKY da take kare umma, saukar DG yaji abayansa, wanda hakan ya tilasta masa yin wani wawan ihu, nanfa kurata suka shiga aikinsu, ihun maza da mata kawai kake ji, nikuwa amarya na samu sai zura mata DG nake tana ihu, aikin kurata yayi tsamari domin kuwa aje DG sukai suka fara karyawa, duk wanda aka karya sai asashi a mota,

Amarya tayo waje aguje na bita tana zuwa tsakiyar layi nasa kafa na daki kafafunta tuni zube ta kasa tashi domin da alama itama ta karye, mutane sun zagayemu anrasa wanda zaice yi hakuri, motar abba ta faka, abba yafito da sauri yaxo yarikeni, wanda hakan yasa kurata tsayawa da aikinsu, amarya tasa hannu tarike kafar abba, abba yasa aka dauki amarya aka kaita gidan yan uwansu suma sauran can aka kaisu, suka kira mai dori yabisu daya bayan daya, Mukuwa muka dawo sabuwar rayuwa. Inda abba yasa akayiwa umma da Ni oder ta motoci guda biyu, ita kuwa Phateema aka bata motar amarya (Toyota venza) dama amarya bata taba hawa ba.

Umma takira yaya Mujaheed tayi mai maganar aure, ya sunkuyar da kai domin bashi da ko budurwa, umma tace kayi shiru yace umma ai bawata tsayayya, Phateema tayi caraf tace ga RUKKY yajuyo na harareta, umma tace yauwa kanwarka tayi maka zabi, aikuwa haka akai tuni aka sanar da iyayenta, Soyayya ta kulli, har aka sa rana amma ba asa da yawaba, don haka tuni ranar biki taxo aka sha gagarumin biki, abba yagina sabon gida su umma suka koma, shikuma shida amaryarsa Sukai barreck, rayuwa ta dawo mana sabuwa, Abba yaje gidan amarya, yana shiga yagata zama abin tausayi, ta taso tana rusa kuka tana neman gafara abba baiyi wata-wata ba ya mika mata ta kaddar saki, yajuya ya fita, amarya tabiyoshi tana neman gafara, amma ina tuni yashiga mota ya yo gida domin duk duniya ba wadda yatsana sama da amarya, kuma ba wadda yakeso sama da umma da “ya”yanta.

Idan su umma suna zaune takan tunawa abba abinda yafaru cikin wasa amma abba sam baya so, Yaya Mujaheed shikuwa da RUKKY ta soyayyar kawai suke shekawa. Ita kuma Phateema Bbu Maganar Aure tacigaba da karatun ta, Ni kuma mungama Exam Munajiran Fitowar Sakamako.

THE END🔥
Wannan Shine Qarshen Labarin.

DARASI

Komai yayi farko yanada Qarshe, Hakazalika zalunci baya dorewa.

Mungode Sosai🙏

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Hussaini Shitu says

    Labari yayi dadi

  2. MUSA YAKUBU says

    Masha Allah gaskiya labari yayi ma’ana Allah kara basira

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »