Yadda Zaa Magance Cutar Mura

0 850

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ga masu fama da matsalar mura ko sarkewar makoshi ko toshewar makoshi ko dai wata lalura a makoshin ko murya ta kasa fita yadda ake bukata sakamakon mura ko tari ko dai wata cutar dabam.

A samu wadan nan abubuwan kamar haka:

1-Citta
2- Kurkum
3- Lemon tsami
4- Sassaken Marke ( Danye ko sabon diba, ba wanda ya dade a ajiye ba)
5-Zuma

Sai a tafasa Citta, Lemon tsami ( har bawon), Sassaken Marke da Kurkum, idan sun tafasa sai a tace a sanya zuma daidai gwargwado sai a rika shan kofi daya da safe, da rana ma a tafasa sai a sha, da daddare ma a kara tafasawa a sha har sai lalaurar ta tafi cikin Hikimar ALLAH.

Insha ALLAH wannan hadin bugu da kari yana karawa garkuwar jiki karfi, yana tacewa mutum jini daga kwayoyin cututtuka, kuma ya kashe duk wata ƙwayar cutar da take kawo matsalolin makoshi da gabobin mutum.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »