Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Bakwai (67)

0 536

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Bayan an tashi daga makaranta ne, sai Labeeba ta isa gida har ta sanarwa da mahaifiyarta irin gagarumar muhadarar da ake shirin yi a makarantarsu dake bayani akan KAMBUN-BAKA da kuma HASSADA.

Ummu Labeeba cikin murna da farin ciki take cewa: Alhamdulillah Maasha ALLAH ! Amma gaskiya wannan muhadarar za ta kayatar sosai, domin yana daga cikin abinda malamai yaci suyi ta fadakar da mutane kenan akan haka, don gudun kar bokaye, Mayu, ‘yan bori da Malaman tsubbu suyi awon gaba da mutane suje su lalata musu rayuwarsu da Imaninsu.

Labeeba: Gaskiya kam Umma wannan haka yake, kuma gaskiya idan Abba yadawo ya kamata ki sanar da shi don na san ma zai barki kije tunda ba wajan shashanci, shirme ko shiririta bane, wuri ne da za a fadakar da al’umma abinda yakamata a rayuwarsu.

Ummu Labeeba: Insha ALLAH kuwa zai barni ma naje saboda yana son narika zuwa irin wuraren nan domin mutum xai karu sosai.

Jimawa kadan kenan sai ga Abu Labeeba nan ya dawo har Ummu Labeeba kuwa ta sanar da shi, yayi murna sosai yana cewa: Ai insha ALLAH tare ma za muje saboda abin zai kayatar sosai kuma za a fadaka, saboda aikata fayyacewa mutane maganar Kambun-baka da hassada saboda wasu da yawa suna ganin ai Kambun-baka maita ce alhalin kuwa ba haka bane Maita dabam Kambun-baka shi ma dabam.

Ummu Labeeba: Allah sarki, ina ji ma wallahy da yawan wasu mutanen da ake tsangwama, ake tuhumar su da maita ma ba Mayun bane Kambun-baka ne da su kawai rashin sanin bambancin ne ke sanya ayita laqa musu maita.

Abu Labeeba: Kwarai kuwa, ai yanzu halin da ake ciki kenan, al’ummar mu da yawa ba ma iya fayyace bambancin dake tsakanin Maita da Kambun-baka, matsalar shi ne: Sau da yawa aikinsu ko ince tasirinsu a jikin mutane ne ke zuwa kusan iri daya sai ayita ganin kamar ai Maita ce wasu ma basu san Kambun-baka ba sai dai maita kawai.

Labeeba: Allah sarki, ai na san insha ALLAH a wurin muhadarar nan za a kara fayyacewa al’umma bayanin nan daki-daki saboda kowa ya fahimci bambancin da kuma matsayin kowanne a shari’ar Allah.

(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji ci gaban bayanin)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »