Labeeba take amsawa mahaifiyarta da cewa: Umma kenan, ai dama ni ba wai na dorawa kaina wata damuwar bace, na dai yi Imani akan Insha ALLAHu Ubangijina yana sane da dukkanin halin da nake ciki, kuma zai kawo min mafita cikin hikima da yardarSA tunda ina kyautata masa zato.
Ummu Labeeba: Allah Sarki diyata, ina matukar alfahari da ke saboda irin wannan tauhidin da kika rike a zuciyarki kuma kike kokarin dabbaka shi a zahiri, ALLAH yashiga cikin lamurran ki.
Labeeba: Aameen ya Hayyu ya Qayyum. Kuma Umma ita Huda din ta nuna min gidanta har take cewa idan har nasamu lokaci tana bukatar nakawo mata ziyara.
Ummu Labeeba: Owk, ba matsala Insha ALLAHu, Allah yakaimu da rai da lafiya, kinga bari dai Abbanki ya shigo shi ma sai kiyi masa bayanin, na san ba hanaki zuwa zai yi ba, kinga sai kije idan kin samu lokacin ko.
Labeeba: Masha ALLAH, ina godiya sosai Umma na. ALLAH yakaimu lafiya.
Jimawa kadan kenan sai ga Salaha nan ta shigo gidan su Labeeba, tayi sallama suka amsa, ta samu wuri ta zauna sai take cewa:
“Wato Ummu Labeeba kinga katin gayyatar daurin auren diyar yayata wacce na kaita wurin mai maganin nan da nake baki labari, yanzu sati mai zuwa ne ma za a daura mata aure.”
Ummu Labeeba tayi murmushi take cewa: Allah yasanya albarka da alkhairi kuma ALLAH yabasu zaman lafiya. Ai wannan lokacinta ne yayi mu ma muna jiran na Labeeba yazo amma ba ta irin hanyar da kike son mu mubi ba.
Salaha: ALLAH Sarki Ummu Labeeba, mayar da wukar, ai ni dama ba wai na zo ne nakara tallata miki mai magani na ba, kawai gayyata nakawo miki ne.
Ummu Labeeba: Ai na sani nima saboda nakara jaddada miki mataki na ne, don har kwanan gobe muna kan cewa ba za mu taba yin Shirka ba akan muna son diyarmu tayi aure, muna nan dai muna jiran hukuncin Allah saboda muna Addu’a tare da kyautatawa ALLAH zaton cewa nan kusa ko nesa inda Labeeba na da rabon yin Aure anan duniya za tayi Insha ALLAHu.
(Insha ALLAHu a rubutu magana za muji cigaban bayanin.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com