Tarihin Unguwar Atafi Dake Jihar Hadejia Jigawa.

0 1,350

Ruwan Atafi

A masarautar Hadejia dake Arewacin Nigeria akwai wata anguwa wanda ake kiran ta ATAFI, unguwar Allah ya mata ni’ima daban daban, ga ruwa ga sanyi ga bishiyoyi kala kala, ga ciyayi koraye, ga kuma kudan zuma mai tarin yawa, shiyasa idan mutane sunje basa son tafoya

A tarihin mutanan Hadejia mutanene mayaka, jaruman gaske, wanda suke batsoro a tattare da su ko kadan, masarautar ta yaki garuruwa da dama wanda hattakai takawo su suka yaki turawan mulkin mallaka da suka shigo arewacin Nigeria shiyasa sarkin musulmi yake kiran sarkin HadejiaSarkin Yakin Sarkin Musulmai wanda har yanzu sunan yana bin sa.

Hakan yasa manyan jaruman Hadejia suka taru a fada, suka tattauna akan, yanzu wasu daga cikin su girma ya fara zuwa musu, kuma gashi sune masu maganunnuwa iri iri na jarumta da dai sauran su.

Sai suka ga yakama matasan san da suke tasowa suma su samu, su samu wadan nan maganunnuwa na jarumta da dai sauran su. Haka suka yanke shawara kowa ya kawo lakanin da yake da shi gobe a samo randa a jika a bawa kowa a gari maza da mata, babba da yaro ya sha.

Anan suka ga randa tayi kadan, gashi lokacin ba abenda yafi randa girma, a cikin su wasu suka bada shawara mai zai hana aje ATAFI tunda waje ne mai ni’ima ga ruwa da yake taruwa a wajan a tona rami kato a jika kowa yazo yana sha.

A hakan aka yadda, washe gari tayi kowa ya kawo abinda take da shi aka je ATAFI aka tona rami aka jika maganunnuwa gaba daya, aka bash shi yayi kwana 3 zuwa 7 sannan kowa yazo yana sha.

Haka zaluka idan za’a tafi YAKI ana taruwa a nan shugaban rundunar yaki zai fadi salon yakin da za ayi, ayi Addu’oi na samun nasara,sannan a SHA ruwan,ana gama sha sai yace atafi, atafi

Daga nan ne wannan anguwa ta samo suna ATAFI shi kuma ruwan sai ake kiran sa da RUWAN ATAFI

Daga Shafin Hadejia Emirate

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »