Takaitaccen Tarihin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar

0 3,272

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Atiku Abubakar GCON (an haife shi ranar 25 ga watan Nuwamba alif  1946), ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa. Ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar Najeriya na 11 daga alif 1999 zuwa 2007 a karkashin shugabancin Olusegun Obasanjo. A  jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).

A shekarar alif 1998 aka zabe shi a matsayin  gwamnan jihar Adamawa. Amm kafin rantsar dashi, dan takarar shugaban kasa  Olusegun Obasanjo  ya zabe shi a matsayin matemkin sa. Don yinkurin su na   lashe zaben  Fabrairun alif 1999,  an rantsar da Atiku a matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya na biyu da aka zaba ta hanyar dimokradiyya a ranar 29 ga watan Mayun shekarar alif 1999.

Atiku ya tsaya takara a jam’iyyar Action Congress (AC), bayan da ya fice daga PDP saboda Matsalar da yasamu da Obasanjo. Atiku Abubakar ya fadi zaben, inda ya zama na uku bayan Umaru Yar’Adua da Muhammadu Buhari na Jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).

Atiku Abubakar shi ne wanda ya kafa kamfanin Intels, wanda ke sana’ar samar da man fetur, tare da gudanar da ayyuka da dama a Najeriya da kasashen waje. Shi ne wanda ya kafa kamfanin Adama Beverages Limited, da Jami’ar Amurka ta Najeriya (AUN), duk a Yola, Adamawa.

Rayuwar Sa

An haifi Atiku Abubakar ne a ranar 25 ga watan Nuwamba shekarar alif 1946, ga wani Bafulatani mai fatauci kuma manomi Garba Abubakar da matarsa ​​ta biyu Aisha Kande a kauyen Jada na jihar Adamawa. Atiku Abubakar ya zama daya tilo a wajen iyayen sa a lokacin da kanwarsa ta rasu yana karami, Mahaifin Atiku da mahaifiyarsa sun rabu kafin mahaifinsa ya rasu a shekarar alif 1957 kuma mahaifiyarsa ta sake yin aure.

A ƙarshe, mahaifiyarsa ta mutu a cikin shekara alif 1984 saboda ciwon zuciya. Atiku Abubakar ba zai iya fara makaranta ba a lokacin da ya kamata domin mahaifinsa yana  da adawa ilimin kasashen yamma. Lokacin da aka lura d Atiku ba ya zuwa makaranta, an kama mahaifinsa aka daure shi har sai da ya biya tara, Sakamakon haka Atiku Abubakar ya samu rajista a makarantar firamare ta Jada yana dan shekara takwas.

Bayan kammala karatunsa na firamare, Atiku ya samu shiga makarantar sakandire ta lardin Adamawa dake Yola a shekarar alif 1960. Daga nan ya kammala karatunsa na sakandare a shekarar 1965 bayan ya rubuta jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma.

Daga nan Atiku Abubakar ya zarce zuwa Kwalejin ‘yan sandan Najeriya da ke Kaduna. Ya bar kwalejin zuwa matsayin jami’in haraji a ma’aikatar kudi ta yankin daga baya ya samu shiga makarantar  tsafta da ke Kano  a shekara alif 1966.

  • Atiku Abubakar
  • Wazirin Adamawa

A shekarar alif 1967 ya kammala da matakin Difuloma. A wannan shekarar ne Atiku Abubakar ya samu gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello ta fannin shari’a, ya kammala karatunsa a shekarar 1969 kuma ya samu aiki a Hukumar Kwastam a Najeriya a wannan shekarar.

Karatunsa

Mahaifinsa ya yi adawa da ra’ayin ilimin Yammacin Turai, kuma ya yi ƙoƙari ya hana Atiku Abubakar shiga makarantar . Lokacin da gwamnati ta gano cewa Atiku ba ya zuwa makarantar, mahaifinsa ya yi kwanaki a gidan yari har sai da mahaifiyar sa Aisha Kande ta biya tarar,

Atiku Abubakar yana dan shekara takwas ya shiga makarantar firamare ta Jada a shekarar alif 1960, ya samu gurbin shiga makarantar sakandire ta lardin Adamawa da ke Yola inda ya yi fice a fannin Turanci da adabi, ya yi gwagwarmaya da Physics da Chemistry da Mathematics. Ya kammala karatunsa da takadar WASSCE/GCE a  shekarar alif 1965.

Bayan kammala karatunsa na sakandare, Atiku ya yi karatu na dan lokaci a Kwalejin ‘yan sanda ta Najeriya da ke Kaduna. Ya bar kwalejin ne a lokacin da ya kasa gabatar da sakamakon lissafin a karatunsa na sakandare, ya yi aiki a takaice a matsayin jami’in haraji a ma’aikatar kudi ta yankin, inda ya samu gurbin shiga makarantar tsafta da ke Kano a shekarar alif 1966. Ya kammala da  Diploma a cikin shekarar alif 1967, bayan zama Shugaban Ƙungiyar ɗalibai na wucin gadi a makarantar.

A shekarar alif 1967 ya shiga digiri  na shari’a a Cibiyar Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello, inda ya samu tallafin karatu daga gwamnatin yankin. Bayan kammala karatunsa a shekarar alif 1969, lokacin yakin basasar Najeriya, ya samu aiki a hukumar kwastam ta Najeriya.

Aurensa Da Iyalansa.

Atiku Abubakar yana da mata hudu kuma yana da ‘ya’ya 28, A lokacin da yake Idi-Iroko, Atiku ya hadu da Titilayo Albert ‘yar shekara sha tara, wacce ya aura a asirce a watan Disamba alif 1971, a Legas, A ranar 26 ga Oktoba alif 1972, Titilayo ta haifi yarinya mai suna Fatima daga baya ta haifi Adamu da Halima da Aminu.

A watan Janairun alif 1979, ya auri Ladi Yakubu a matsayin matarsa ​​ta biyu, har yake cewa  “Ina so in fadada gida na, na ji kadaici sosai tun ina karami ba ni da kanne kuma ba ni da ‘yar uwa, bana son ‘ya’yana su zaman kadaici kamar yadda na yi, shi ya sa na auri mata fiye da daya. Matana ’yan uwana ne, abokaina, kuma mashawartana kuma suna taimakon juna,” in ji Atiku Abubakar. Yana da ‘ya’ya shida tare da Ladi: Abba, Atiku, Zainab, Ummi-Hauwa, Maryam da Rukaiyatu.

A shekarar alif 1983 ya auri matarsa ​​ta uku, Gimbiya Rukaiyatu, diyar marigayi Lamidon Adamawa, ta haifi Aisha, Hadiza, Aliyu Asmau, Mustafa, Laila da Abdulsalam.  Matarsa ​​ta hudu, Fatima Shettima, ta biyo baya a shekarar alif 1986 Fatima ta haifi ‘yarta ta farko Amina (Meena), Mohammed da tagwaye Ahmed da Shehu, Zainab da Aisha sai ‘yarta ta karshe Hafsat.

Daga baya Abubakar ya saki Ladi, inda ya ba shi damar auren,  matarsa ​​ta hudu wato, Jennifer Iwenjiora Douglas.

Farkon Siyasarsa.

Atiku Abubakar ya fara shiga harkar siyasa a farkon shekarar alif 1980, lokacin da ya yi aiki a bayan fage kan yakin neman zaben Gwamna Bamanga Tukur, wanda a lokacin ya kasance Manajan Daraktan Hukumar Tashoshin Ruwa ta Najeriya.

Ya yi kaurin suna wajen neman kuri’u a madadin Tukur, sannan kuma ya bayar da gudunmawa ga yakin neman zaben. A gab da karshen aikinsa na Kwastam ya hadu da Shehu Musa ‘Yar’aduwa, wanda ya kasance na biyu a gwamnatin mulkin soja a mulki a tsakanin  alif 1976 zuwa alif 1979.

Yar’adua ya jawo Atiku Abubakar cikin tarurrukan siyasa. A shekarar  alif 1989 aka zabi Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Front of Najeriya (PFN) na kasa, kungiyar siyasa karkashin jagorancin ‘Yar’aduwa, domin shiga shirin mika  da shugaban kasa Ibrahim Babangida ya kaddamar.

Jam’iyyar Peoples Front ta Najeriya ta hada da ‘yan siyasa irin su Umaru Musa Yar’adua, Babalola Borishade, Bola Tinubu, Abdullahi Aliyu Sumaila, Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Sabo Bakin Zuwo.

Zamansa Mataimakin Shugaban Kasa.

An rantsar da Atiku Abubakar a matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun shekarar alif 1999.

A shekarar alif 1999  tare da mataimakin shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma suka kaddamar da hukumar hada kan Najeriya da Afirka ta Kudu.

Girmamawa Da Kyaututtuka.

A shekarar alif 1982 Sarkin Adamawa Alhaji Aliyu Mustafa ya ba Atiku Abubakar sarautar Turakin Adamawa. A baya dai an kebe wannan sarauta ne ga basaraken da sarki ya fi so a fadar, kasancewar mai rike da mukamin shi ne ke kula da harkokin cikin gida na masarautar.

A watan Yunin 2017 ne aka baiwa Abubakar mukamin sarauta na Wazirin Adamawa, inda a baya na Turaki aka mayar wa dansa Aliyu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »