Takaitaccen Tarihi Alh. Aminu Dantata

0 2,438

Aminu Dantata na ɗaya daga cikin hamshaƙan ƴan kasuwa dake jihar Kano a Najeriya kuma mai taimakon jama’a wanda yana ɗaya daga cikin masu tallafa wa Gidauniyar Jihar Kano, a asusun bada tallafi wanda yake tallafa wa ilimi tare da bayar da tallafi ga ƙananan ‘yan kasuwa a Kano Shi ne shugaban rukunin kamfanonin wanda ke kula da kadarorinsa da sauran harkokin kasuwanci.

Aminu Dantata shine ya kafa kamfanin Express Petroleum & Gas Company Ltd kuma ɗaya daga cikin jagororin bankin Jaiz dake Najeriya. A shekarar alif 1978, ya kasance memba na National Movement, kungiyar da daga baya ta rikide zuwa jam’iyyar National Party of Nigeria (NPN.

Rayuwar Sa.

An haifi Aminu Dantata a dangin Alhassan Dantata, shi ne ɗa na goma sha biyar a cikin  yara goma sha bakwai. Daga alif 1938 zuwa alif 1945, ya halarci makarantar firamare ta Dala sannan ya gama karatunsa ta hanyar karatun gida a wata makaranta mai zaman kanta da mahaifinsa ya gina.

Bayan ya kammala karatun sa, ya shiga harkar kasuwanci na kamfanin haɗin gwiwa na mahaifinsa, wato Alhassan Dantata & sons a shekarar alif 1948 a matsayin mai siyar da kayan amfanin gona sannan kuma ya yi aure a shekarar alif 1955 ya zama manajan kasuwanci na gundumar Sokoto a Shekarar alif 1955 kuma a shekarar ce lokacin da mahaifinsa ya rasu kuma daga baya aka raba hannun jari ga yaran.

A shekarar alif 1958, Dantata ya zama mataimakin manajan darakta na kasuwanci tare da yayansa Ahmadu, shi ne MD. Lokacin da Ahmadu ya rasu a shekarar alif 1960, Dantata ya zama shugaba.

A tsawon shekaru, Aminu Dantata ya fadada harkokin kasuwancin da zuwa sassa daban-daban na harkokin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

A farkon shekarar alif 1960, Aminu yana da kamfanin gine -gine wanda ya samu tallafi daga sabuwar gwamnati mai zaman kanta a Najeriya, an ba kamfaninsa kwangilar gina wani bangare na Makarantar Sufurin Jiragen Sama a Zariya.

A shekarar alif 1961, yana cikin wasu yan kasuwa guda uku a matsayin wani bangare na kungiyar masu fafutuka ta fuskar tattalin arziki guda 23, wato manufa ta farko da wata gwamnati mai cin gashin kanta ta aika a fadin  duniya a Najeriya.

A shekarar alif 1964, yana daga cikin shugabannin kwamitin gudanarwa na bankin bunkasa masana’antu ta Najeriya. A shekarar alif 1968, an nada Aminu kwamishinan raya tattalin arziki, kasuwanci da masana’antu na jihar kano karkashin mulkin Audu Bako, yana kan mukamin har zuwa alif 1973.

Bada Gudunmawa:

Dantata ya bayar da gudummawar kudade da gine-gine ga cibiyoyi daban-daban da ke kewayen Kano. Ya baiwa asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano gudummawar cibiyar Alhassan Dantata Haemodyalysis Centre. Kuma shine shugaban jami’ar Al-Qalam na farko a Katsina.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »