Amfanin Bishiyar Tunfafiya Ga Lafiyar Jikin Dan Adam.
Ita dai bishiyar Tunfafiya, mutanen da suka gabata a shekarun baya su suka fi amfani da ita wajen maganin wasu cutuka dake damun su a wannan lokacin.
Sai dai kuma a cikin wannan zamani da muke ciki mutane da yawa basu damu da ita bishiyar ba Kasan cewar ɗaukar ta da mukai cewa duk inda bishiyar Tunfafiya take to matattarar Aljanu ce a wurin, don haka ne ma ya sanya Bama kusantar ta musamman da tsakar rana ko da Daddare.
Abin da kuma wasu mutanen basu sani ba shi wannan bishiya ta Tunfafiya tana da matuƙar muhimmanci ga lafiyar mu kama tun daga icenta, sauyoyin ta, ganyenta, fulawar jikinta, da kuma ƴaƴan ta.
Insha Allahu a wannan bayani da zamuyi zamu kawo muku muhimmancin amfanin da wasu sassan jikin Bishiyar Tunfafiya.
GANYEN TUNFAFIYA:
- CIWON GAƁOƁI. Za’a samu ganyen Tunfafiya sai sanya shi a garwashin wuta a dinga fifita garwashin har ganyen ya ɗauki zafi sai dinga dannawa a wurin dake da cewa Kamar: Ciwon Gaɓoɓi, ciwon tafin Ƙafa, ciwon sanyin ƙashi da sauran duk wani nau’i na ciwon ƙashi.
- KURAMAN TAKA TA DALILIN WATA CUTA. Ana samun ganyen Tunfafiya wanda ya fara canza kalar rawaya ( Yellow ), sai a tafasabshi sosai idan yayi sanyi sai a dinga wanke kunne dashi, yana maganin Kurman taka ta dalilin wata cuta.
- CIWON BASIR MAI TSIRO; Za’a samu ganyen Tumfafiy said a konashi sama sama sai a sanya man basilim akan ganyen sai a danga danawa akan inda Basir din ya fito insha allahu zai koma kuma ya warke sarai.
ƘWALLON TUNFAFIYA:
- MAGANIN MAYU; Ana cin ƙwallon tunfafiya don maganin Mayu ko sihiri. Zaku samu furen Tunfafiya saiku bude cikin sa akwai kwallaye a ciki to su zaku dinga ci.
FUREN TUNFAFIYA:
Furen Tunfafiya
- YADA ZA’A MAGANCE ƊAUKAR CUTA YAYIN SADUWA MACE KO NA MIJI. Ana shanya furen Tunfafiya indan ya bushe sai a da kashi yayi laushi sai a dinga ɗiban girgije ɗaya na cokali a dinga sha a Nono; shi kuma yana maganin rashin ɗaukar duk wata cuta da ake ɗauka a wurin saduwa mace ko namiji.
- MAGANIN TSUTSAR CIKI; Haka kuma ana samo furen Tunfafiya a markaɗashi a tafasa a tace shi a samu kofi a zuba shi a zuba zuma a sha, yana kashe Tsutsar ciki.
MADAARAR TUNFAFIYA:
- MAGANIN CUTUTTUKAN FATA; Ana matse madarar Tunfafiya sai a haɗa da man Kade a juye su a yar ƙaramar roba a dinga shafa wa bayan anyi wanka yana maganin Cututtukan fata kamar kurajen Jiki, ƙaiƙayin Jiki, da sauran cututtukan fata.
- MAKERO; shi kuma za’a kankare makeron idan ya fara jini sai a ɗiga madarar ruwan tunfafiya a kai duk bayan kwan biyu, zai warke Insha Allahu.
DAN TUNFAFIYA:
- MATSALAR ƘWAƘWALWA KO CIWON KAI; Ana cire barkonan tsohuwa dake cikin ɗan tunfafiya a zubar dashi sai a shanya dan idan ya bushe sai a daka shi yayi laushi ba’a shansa saidai ayi shaƙe ta hanci idan an shaƙa ɗin yana magani kamar: mai fama da matsanancin ciwon kai, mai ciwon hauka da duk wata matsala dake cikin ƙwaƙwalwa.
Budaden Kwallon Tunfafiya
ICEN KO ƁAWAN TUNFAFIYA:
- MAGANIN CIWON HAƘORI; Ana samo icen ko kuma ɓawon Tunfafiya sai a ɗora shi a garwashin wuta hayaƙin dake fita sai a dinga shaƙar hayaƙin. Shi kuma yana maganin ciwon Haƙori da kuma tarin fuka.
- CUTAR KUTURTA; Sannan ana samun ɓawon Tunfafiya a dake ya daku sai a hadeshi da man kaɗe a dinga shafa wa a inda cutar Kuturta ta bayyana.
Salam.baraka da warhaka Muna gudiya da dinbin ilimai da akibamu Allah ya sakada alhairi Allah ya qara basira