Alh. Auwalu Abdullahi Rano wanda aka fi sani da AA Rano an haife shi ne a ranar 9 ga watan Yuni alif 1944 a cikin al’ummar Hausa-Fulani a wani kauye da ake kira Lansu a karamar hukumar Rano a Jihar Kano da ke Najeriya.
Yayi karatunsa na primary a Lansu Yamma, sannan yayi karatunsa na sakandire a karamar hukumar Rano.
hamshakin attajirin nan mai arzikin man fetur, ya fara sana’ar sayar da Alkama, Wake, Gyada sannan ya fara saida kanazir daga baya ya hada da Gas daga nan kuma ya fara saida man fetur da kuma rabar dashi kadan kadan a shekarar alif 1994. A matsayinsa na matashin dan kasuwa, ya yi mafarkin zama jagora a bangaren masana’antar man fetur ta Najeriya, ta haka ya samar da man fetur da ɗorewar kudaden shiga da bunƙasa a cikin ƙwaƙƙwaran ƙalubale na ƙasa da ƙasa na masana’antar man fetur ta Najeriya.
Ya gina kantunansa na farko a jihar Kano a shekarar alif 1996, sannan ya kafa kamfanin A. A Rano Nigeria Limited a shekarar 2002.
A ‘’yan shekaru, kamar da wasa, A.A Rano Nig.Ltd ya bazu zuwa lungu da sako na Najeriya tare da gidajen mai da yawa a fadin kasar.
Tallafawa Jama’a
Baya ga kasancewarsa hamshakin dan kasuwa, AA Rano hamshakin mai ba da taimako ne. Ya kafa fitacciyar gidauniyar AA Rano, kungiya mai zaman kanta, kuma ta maida hankali kan ayyukan ci gaban al’umma da suka hada da lafiya, ilimi, samar da ruwan sha, karfafa matasa da mata.
AA Rano shi ne ya kirkiri Darul Sunnah, wanda ke cikin Jihar Kano. A wannan cibiya ana koyar da ilimin addinin musulunci, ana gudanar da tarukan karawa juna sani da shirye-shirye a kan addinin musulunci da malamai kamar su Sheik Ibrahim Daurawa.
Gidauniyar AA Rano
Haka kuma, shi ne shugaban gidauniyar AA Rano, gidauniyar da ke tallafa wa dalibai da kudaden karatu, da kuma biyan majinyata kudin magani ko tiyata.
Ya zama al’ada AA Rano yana rage farashin man fetur a gidajen mansa a duk watan Ramadan domin saukakawa al’umma.
Masha Allah