A wannan rubutun zamu kawo muklu bayanin runduna ta Shida da ta bakwai, wacce ta shida ta kasance a watan Rabiul Auwal a bisa Jagorancin Muhammadu Dan Muslimata ita kuma runduna ta Bakwai Bisa Jagorancin Zaidu Dan Harisatu.
RUNDUNA TA SHIDA
A cikin watan Rabi’ul Auwal ne labari ya zowa shugaban halitta cewa wasu daga cikin kafirai sunyo sansani domin su kwace dabobbin wasu musulamai a wani gari da ake cewa haifa’u, wani kauye ne a kusa da madina, su kuma kafiran suna wani kauye da yake da suna Kassatu mil ashirin da hudu ne daga madina.
To koda wannan labari ya zowa shugaba sai ya samu mutum goma daga cikin sahabbai a bisa jagorancin Muhammadu Dan Muslimata ya tura su domin bada kariya ga ‘’yan uwanmu musulmai da kuma fito na fito da azzluman kafiran wannan yanki.
To andade ana fafatwa tsakanin wadannan sahabbai na manzon ALLAH {saw} da kuma wadannan miyagun kafirai a inda su kafiran suka samu nasarar kasha duk kan sahabban nan guda goma amma banda shi muhammadu wato kwamandan yakin amma shima a zaton su sun kashashi saboda raunukan da yasamu.
To bayan sun tafi sai ya farfado ya dawo gida ya bawa manzon Allah labarin yanda al’amarin ya kasance, to sai manzo Allah ya dan jinkirta musu kadan sai acikin watan Rabi’ul Akhiri sai yaske tura wata rundunar a karkashin jagorancin abu Ubaidatu Dan Amiru domin yaje shima yayi maganin wayannan yan iska, to amma meke faruwa tun kafin su isa wannan gari tuni kafirai sun ranta a na kare gaba dayansu sun gudu.
Koda abu Ubaidatu yaga haka sai suka shiga garin suka koro dukan dabobin garin suka taho gida.
RUNDUNA TA BAKWAI
Wata rana Zaidu Dan Harisatu ya dawo daga saye da sayarwar sa daga garin sham sai ya hadu da wasu kafirai yan kabilar bani fazazata, mazauna wani kauye da ke cewa Wadilkura, sai suka tare Zaidu Dan Harisatu suka kwace duk wani abu da ya sayo a karshe ma dai sun so su kasha shi ALLAH ne ya kareshi daga sharinsu.
Don haka sai yazo ya sanar da Manzon ALLAH {saw} abin da suka yi masa .
Sai Manzon ALLAH {saw} ya tura Zaidu tare da wasu sadaukai suka nufu wannan kauye na wadannan yan fashi n kafirai domin su dauko fansar abin da sukayiwa Zaidu.
Ita dai wannan rundun koda taje garin sai suka zagaye shi suka karkashe mafiya yawan mutanan garin harma aka ribato matar sarkin garin suka taho da ita bayan sun tagaiyara garin baki daya.