Kurajen Kazuwa.
Ga duk wanda yake da kurajen kazuwa ko wasu kuraje ko miki,ya samu ganyen zaitun ya kirbashi ya hada da garin habbatussauda yarika shafawa a Wajen har ya warke.
Ciwon Kunne.
Ga duk mai fama da ciwon kunne,to yabari idan zai kwanta bacci sai ya hada man zaitun dana habbatussauda yana digawa a kunnen Insha Allah za’a samu saukin ciwon.
Cutar Kyasfi.
Duk mai fama da kyasfi a fuska ko a jikinshi to yasamu ganyen zaitun busasshen,adakashi yazama gari sai a kwabashi da man zaitun,ya cakuda yadinga shafawa Wajen da kyasfin yake Lokacin da mutum zai kwanta bacci sai ya wanke insha Allah shima za’a dace.
Shafar Aljanu.
Duk mutumin da yakeson yarabu da Aljanu to yarika amfani da man zaitun da habbatussauda saboda Aljanu basa sonshi.
Ciwon Dan Yatsa Dan Kakkare.
Idan mutum yana fama da dan kakkare,yasamu man zaitun ya kwaba da lallen hausa,sai a karanta Ayatul kursiyyu sau bakwai atofa a lallen akuma tofa a hannun sai akunsa lallen a hannun insha Allah shima za’a samu waraka da ikon Allah.
Ciwon Nono.
Duk matar datake fama da ciwon nono wanda yatoshe baya zuba to ana hada man zaitun da garinsa a shafa a nonon insha Allah kofofin zasu bude.
Motsa Sha’awa Ga Ma’aurata.
Ga masu ƙarancin sha’awa man zaitun yana motsa sha’awa idan akayi amfani dashi lokacin da ake gabatar da wasa.
Ciwon Saifa.
Duk wanda yake fama da ciwon saifa,sai yahada man zaitun da garin habbatussauda da zuma farar saka sai yarika sha insha Allah za’a samu waraka.
Tsutsar Ciki.
Duk mutumin da yake da tsutsar ciki to sai ya samu man zaitun da habbatussauda garin da zuma ya kwabasu yarika sha Insha Allah za’a samu biyan bukata.
Gyambon Ciki (ulcer)
Duk mutumin da yake da gyambon ciki to sai ya samu garin habbatussauda Kamar cokali daya sannan yasamu garin kumasari, da ganyen zaitun mai laushi yajikasu yarika sha har sai ya warke.
Fitsarin Kwance
Duk yaron da yake da fitsarin kwance asamu garin zaitun dana habbatussauda a zuba a nono arika Bashi yana sha, zai daina da ikon Allah.
Aisha Musa Yankara
[…] post Amfanin Man Zaitun Ga Lafiya appeared first on Alummar […]