Sadiya Mohammed wacce aka fi sani da Sadiya Gyale na daya daga cikin jarumar kannywood, an haife ta a ranar 19 ga watan Satumba, shekarar alif 1985.
Sadiya wacce aka haifa a jihar Legas, asalin ta ya fito ne daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
Sadiya tana ɗaya daga cikin waɗanda tauraron su ya haska a masana’antar Kannywood don haka tana samun nasarori da dama. Tasamu farin jini a masana’antar kasancewar iya tafiyar da duk wani bangare da aka sakata a shirin fim.
Haka kuma Sadiya Gyale tasamu wani farin jinin kasancewar ta ba mai son nuna tsaraicin jikinta ba.
Sadiya ta shiga masana’antar shirya finafinan Hausa a shekarar 2001 inda ta fara fitowa a fim ɗin ta na farko mai sun Gyale.
Sannan ta kuma fito a wasu sanannun fim kamar su Baƙar Ashana, Dan Yola, Duniyar, Gidan Gado, Gwanaye, Ƙauna, Jamhuriya, Kishiya. Da dai sauran wasu da dama.
Sadiya ta ɗan bar fim na wasu lokuta daga baya kuma ta dawo da katin gayyatar aurenta.
Gyale tayi aure a ranar 10 ga watan Afrilu a shekarar 2015 inda ta auri Bar. Abubakar Muhammad, sannan ta fito a shekarar 2015 ɗin.
[…] post Takaitaccen Tarihin Sadiya Muhammad Gyale appeared first on Alummar […]