Runduna Ta Biyu, Samun Ganima Ta Farko A Musulunci

1 248

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


Ganima ta farko a addinin Musulunci ita ce wacce aka sameta a cikin wata runduna ta manzon ALLAH {saw} da ya tura ta abisa jagorancin Abdullahi dan Ja’ashin, tare da Jarumai tamanin (80) a cikin sahabbai.

Sai dai kwamadan wannan rundun wato Abdullahi dan Ja’ashim wata rana bayan Manzon Allah {saw} ya idar da sallah isha’I sai yakira Abdullahi dan Ja’ashim, yace dashi, ya kai Abdullahi gobe tun da asuba ina son ganinka kuma kazo cikin shirinka na yaki.

Tun da asuba Abdullahi dan Ja’ashim ya fito da makamansa na yaki, tare da tokobinsa da kayan harbi tun na wacen lokacin.

Bayan manzon allah {saw} ya idar da sallar asuba ya fito daga masallaci sai kawai Manzon Allah {saw} ya ga Abdullahi a tsaye sai Manzon Allah {saw} ya nemi maga takardar sa aka rubuta wata wasika sai Manzon Allah {saw} ya je gurin Abdullahi dan Ja’ashim yace dashi.

“Nashugabantar dakai acikin wadancan sadaukan, sannan sai Manzon Allah {saw} ya juya ga sadukan y ace dasu: Na shugabantar muku da wani mutum daga cikin ku ba don wai yafiku ba, sai dai cewa shi mutum ne wanda yafi kudirewa yunwa da kuma kishirwa.

Shi dai wannan kwamadan baya tsoran mutuwar shahada domin a lokacin da za’a fita yakin Uhudu ga adu’ar da yay kafin ya fita sai ya kebe yace :
“Ya ubangiji gobe idan mun fita yaki kahadani da kafiri wanda yake ji da kansa mai tsananin karfi da iya yaki nikuma zan zare takwabina in yakeshi har ALLAH ya kaddara yin shahadata, idan yakasheni ya datse hancina da kunnena idan na hadu da mahalicci na yace dani: Ya kai Abdullahi garin ya aka yanke maka hanci da kunne? Ni kuma sai ince da Allah madaukakin sarki: Ya Ubangiji anyi min haka ne a gurin yaki domin kada na ki bin umarnin Manzonka”.

Sai gashi kuwa Allah madaukakin sarki ya karbi addu’ar wannan sahabi mai girma domin kuwa wannan sahabi ansameshi bayan angama yaki anganshi mai yankaken kune da hanci, wani kafiri mai suna Abul Hikami shi ya kasha shi.

To mai sararo bayan Manzon ALLAH {saw} ya gama nasihar sa ga wannan runduna sai ya mika wata takarda ga shugaban wannan runduna wato Abdullahi dan Ja’ashim, manzon ALLAH {saw} yace kada kubude wannan takarda har sai kaje wani wuri da ake cewa Nahlatu, shi wannan wuri yannan a tsakanin makka da Da’ifa.

Don haka sai wannan rundun ta tafi, sai da sukayi tafiyar sati biyu sannan wannnan sahabi ya bude wannan takarda ta Manzon ALLAH {saw} sai yaga rubutu “Idan ka duba wannan takardar to kaci gaba da tafiya har sai kaje Nahlatu, to ka binciko mana labarin Ƙuraishawa.

To bayan ya karanta wannan takarda ta Manzon ALLAH {saw} sai yagayawa sauran jama’a gaba daya abin da ta kunsa gaba daya sahabbai suka ce mu dai munyi biyayya ga Allah da kuma Manzonsa kuma mun bika muje duk inda yakamata, amma an samu wasu daga cikin sahabbai su biyu da suka juya suka shiga daji neman rakuminsu wato Sa’ad dan abi Wakkas, da Utbau dan Gazwana.

Abdullahi dan Ja’ashi ya ce: yaku yan uwa musulmai duk wanda yake da burin shahada to ya biyoni muje duk wanda yake tsoran mutuwa to ya juya, ni dai na wuce domin zartar da umarnin Manzon ALLAH {saw}.

Nan take ya wuce shi da sauran yan tawagarsa har suka je daidai Nahlatu inda Manzon allah yace insun je su tsaya. Suna daidai wannan wurin ne sai ga wani ayari na Ƙuraishawa sun zo zasu wace dauke da abubuwan jin dadi da kayan kasuwancin su sun dawo daga Da’ifa, a cikin wannan tawaga ta Ƙuraishawa, akwai Umaru dan Habarani, akwai Usman dan Migiratu akwai Naufilu dan Mugira akwai Hakamudan Haisana, kafin su ƙara so sai Abdullahi dan Ja’ashim ya yanke shawarar afkawa wadannan kafirai haka kuwa akaiyi domin musulmai sunyi nasara a cikin wannan fafatawa harma suka chafke Usman dan Hakamu, suka kasha Usman dan Habarani suka kara rakuma da abubuwan jin dadi kuma wannan itace ganima ta farko da musulamai suka fara rabauta da ita daga makiyansa.

Wasu daga cikin mushurukai sun biyu bayan musulmai amma ALLAH bai sa sun tarar da musulmai bah.

To mai karatu idan baka manta ba akwai sahabbai biyu da suka shiga daji neman rakumi kuma suna cikin neman rakumin nasu wasu kafirai suka yi garkuwa dasu, don haka bayan kafirai sun sami labarin cewa ankama mutanen su sai suka aikawa Manzon ALLAH {saw} cewa suna neman cewa a sako musu mutanensu sai Manzon ALLAH {saw} ya ce dasu a’a baza’a saki mutanensu bah, har sai sun kama sahabban da sukayi garkuwa dasu, wato Sa’ad da kuma Utbatu, to a lokacin da suka sako su sai Manzon allah ya saki nasu mutanen amma ɗaya daga cikinsu ya musulunta, wato Hakamu dan Kaisana shi ,kuwa Usmanu bai musulunta ba ya koma Makka yaci gaba da bin addini mahaifansa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] post Runduna Ta Biyu, Samun Ganima Ta Farko A Musulunci appeared first on Alummar […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »