Adamu Abdullahi Zango wanda akafi sani da Adam A Zango, Usher ko Gwaska shahararran dan wasan Hausa ne a Kamfanin shirya fina-finan Hausa dake Kano, kuma mai shirya fina-finai, Mawaki, Dan Rawa.
HAIHUWARSA:
An haifi Jarumi Adam A Zango wanda akan yawan kirashi da (Usher) ko (Gwaska), a ranar 1 ga watan ogas din shekarar alib 1985, a karamar hakumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, tare da mahaifinsa Malam Abdullahi da kuma mahaifiyarsa Hajiya Yelwa Abdullahi.
KARATUNSA;
Adam A Zango yayi Firamari a shekarar alib 1989 sanan ya gama a shekarar alib 1995, sanan ya fara makarantar sakandire a shekarar alib 1996 sannan ya gama a shekarar 2001.
RA’AYINSA GAME DA KARATU
Adam A Zango bai kammala wata Jami’a ko Polytechnic, domin a cewarsa samun wani kwalin Digiri ko makamancin haka bashine yafi muhimmanci ba matukar mutum zai iya samar da wata gudunmawa a kansa da Alummar da suke tare dashi, kuma ya koyi wani abu daga garesu sannan shima ya sanara dasu wani ilimi dayasani, wannan shine Ilimi.
A cewar Adam A Zango yanda matukar sani akan lamarin rayuwa, kuma ni mai ilimi akan abubuwa da nasani, bawai lallai sai mutum ya mallaki takaddar Digiri ko sama da Digiri ba.
KIDA DA WAKAR ADAM A ZANGO.
Lamarin Adama A Zango akan kida da waka kuwa ya faro asali ne tun lokacin da yana makarantar Sakandire, tun lokacin Adam A Zango yake wakiltar makarantasu.
SHIGA MASANA’ANTAR SHIRYA FINA-FINAN HAUSA.
Adam A Zango yashiga masana’atar shirya fina-finan Hausa a shekarar 2001, a mai kida, rawa da kuma rubuta waka. Sabo da amfaninsa a masana’antar sai ya fara fitowa a fim a matsayin karamin Jarumi, Adam A Zango yayi finan-finai sama da guda Dari (100).
ZAMAN GIDAN YARI.
A 2007 ne dai Adam A Zango aka yanke masa zama a gidan yari sakamakon karya doka da yayi na sakin wani Bidiyo mai suna Bahaushiya.
BAJINTAR DA YAYI WACCE BAZAA MANTA DA ITABA
A watan Oktobar 2019 ne dai Adam A Zango ya biya wasu makudan kudade da sukakai Miliyan Arba’in da Bakwai , ga Maryu don taimakawa karatunsu, kuma yaje har fadar maigirma Sarkin Zazzau Alh. Shehu Idris ya gabatar da kyautar.
Haka kuma a shekarar 2019 ne dai Adam A Zango ya bayyana kansa a wanda yafi kowa tasiri a kasar Hausa.
Allah yakara daukaka adam azango aduniya da lahira