WAYE LAWAN YAHAYA AHMAD
Lawan Yahaya Ahmad na daya daga cikin Jaruman Masana’antar shirya Fina-finan Hausa dake Kano, kuma yasamu shiga masana’antar ne da taimakon Jarumi Ali Nuhu.
HAIHUWARSA
Ana haifi Jarumi Lawan Ahmad a ranar 13 ga watan March din Shekarar Alib 1982, a karamar hukumar Bakori dake jihar Katsina a Najeriya.
KARATUNSA
Lawal Ahmad yayi karatunsa na Firamari a makarantar Nadabo Primary School Bakori, a shekarar alib 1987 zuwa shekarar alib 1993.
Lawal Ahmad yayi karatunsa na Karamar Sakandire a makarantar Gobnati ta Government Day Secondary School Bakori, sanan Sai ya wuce zuwa Makarantar Gobnati ta Sharada dake Kano wato Government Daya Secondary School Sharada, inda a nan ya mallaki takardar shaidar gama Sakandiri wato SSCE.
Lawal Ahmad ya kuma fadada Iliminsa a Boko yayinda ya shiga makarantar Federal College Of Education dake Kano a shekarar 2002 zuwa 2004. Daga nan kuma ya wuce zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule a shekarar 2016.
SHIGARSA MASANA’ANTAR FIM
Jarumi Lawan Ahmad ya shiga masana’antar Shirya fina-finan Hausa dake Kano a shekarar alib 1999, kuma yayi fim dinsa na farko mai suna SIRAD.
Lawal Ahmad ya mallaki Kamfanin shirya Fina-finan Hausa mai suna Bakori Entertainment.
Very good
Umar Hashim
MJKS