Ummi Ibrahim wacce akafi sani da Ummi Zee Zee na daya daga cikin tsofin Jaruman shirya finafinan Hausa dake Kano, kuma mawakiya.
An haifi Ummi Zee Zee a shekarar alib 1989 a Jihar Barno dake Najeriya, mahaifinta Fulani ne sai kuma mahaifiyarta Arab.
Ummi Zee Zee mawakiya ce inda tayi wakoki dayawa, haka kuma Zee Zee batayi wasu finafinai masu yawa ba a masana’antar Shirya finafina Hausa ba.
Zee Zee tasamu lamar yabo akan wani fim mai suna Jinsi, wanda sukayishi tare da Jaruma Fati Washa.